< Zabura 58 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Ku masu mulki tabbatacce kuna magana daidai? Kuna yin shari’a daidai a cikin mutane?
למנצח אל-תשחת לדוד מכתם ב האמנם--אלם צדק תדברון מישרים תשפטו בני אדם
2 Sam, a zuciyarku kuna ƙirƙiro rashin adalci, da hannuwanku kuma kuna tā da hargitsi a duniya.
אף-בלב עולת תפעלון בארץ--חמס ידיכם תפלסון
3 Kai, tun haihuwa mugaye sukan kauce; daga cikin ciki, su lalatattu ne maƙaryata.
זרו רשעים מרחם תעו מבטן דברי כזב
4 Dafinsu ya yi kamar dafin maciji, kamar na gamsheƙan da ya toshe kunnuwansa,
חמת-למו כדמות חמת-נחש כמו-פתן חרש יאטם אזנו
5 da ba ya jin muryar gardi, kome dabarar gwanin mai waƙar zai zama.
אשר לא-ישמע לקול מלחשים חובר חברים מחכם
6 Ka kakkarya haƙoran a bakunansu, ya Allah; ka yayyage fiƙoƙin zakoki, ya Ubangiji!
אלהים--הרס שנימו בפימו מלתעות כפירים נתץ יהוה
7 Bari su ɓace kamar ruwa mai wucewa; sa’ad da suka ja bakansu, bari kibiyoyinsu su murtsuke.
ימאסו כמו-מים יתהלכו-למו ידרך חצו כמו יתמללו
8 Kamar katantanwun da suke narkewa yayinda suke tafiya, kamar jinjirin da aka haifa matacce, kada su ga hasken rana.
כמו שבלול תמס יהלך נפל אשת בל-חזו שמש
9 Kafin tukwanenka su ji zafin ƙayayyuwa, ko su kore ne ko busasshe, za a shafe mugaye.
בטרם יבינו סירתכם אטד כמו-חי כמו-חרון ישערנו
10 Masu adalci za su yi murna sa’ad da aka rama musu, sa’ad da suka wanke ƙafafunsu cikin jinin mugaye.
ישמח צדיק כי-חזה נקם פעמיו ירחץ בדם הרשע
11 Sa’an nan mutane za su ce, “Tabbatacce har yanzu ana sāka wa adalai; tabbatacce akwai Allahn da yake shari’anta duniya.”
ויאמר אדם אך-פרי לצדיק אך יש-אלהים שפטים בארץ

< Zabura 58 >