< Zabura 57 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da muryar “Kada Ka Hallaka.” Ta Dawuda. Wani miktam. Sa’ad da ya gudu daga Shawulu zuwa cikin kogo. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, ka yi mini jinƙai, gama a gare ka raina yake samun mafaka. Zan sami mafaka a inuwar fikafikanka sai masifar ta wuce.
למנצח אל-תשחת לדוד מכתם-- בברחו מפני-שאול במערה ב חנני אלהים חנני-- כי בך חסיה נפשי ובצל-כנפיך אחסה-- עד יעבר הוות
2 Na yi kuka ga Allah Mafi Ɗaukaka, ga Allah, wanda yake cika manufarsa gare ni.
אקרא לאלהים עליון לאל גמר עלי
3 Ya aika daga sama ya kuwa cece ni, yana tsawata wa waɗanda suke fafarata da zafi; (Sela) Allah yakan aika da ƙaunarsa da amincinsa.
ישלח משמים ויושיעני-- חרף שאפי סלה ישלח אלהים חסדו ואמתו
4 Ina tsakiyar zakoki; ina kwance a cikin namun jeji masu cin mutane, mutanen da haƙoransu masu ne da kuma kibiyoyi, waɗanda harshensu suna da kaifi kamar takobi.
נפשי בתוך לבאם-- אשכבה להטים בני-אדם--שניהם חנית וחצים ולשונם חרב חדה
5 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.
רומה על-השמים אלהים על כל-הארץ כבודך
6 Sun shimfiɗa raga don su kama ƙafafuna, damuwa ta sha ƙarfina. Sun haƙa rami a hanyata, amma su kansu suka fāɗa a cikinta. (Sela)
רשת הכינו לפעמי-- כפף נפשי כרו לפני שיחה נפלו בתוכה סלה
7 Zuciyata tana nan daram, ya Allah, zuciyata tana nan daram; zan rera in kuma yi kaɗe-kaɗe.
נכון לבי אלהים נכון לבי אשירה ואזמרה
8 Ka farka, raina! Ku farka, garaya da molo! Zan sa safe yă farka.
עורה כבודי--עורה הנבל וכנור אעירה שחר
9 Zan yabe ka, ya Ubangiji, a cikin al’ummai; zan rera game da kai a cikin mutane.
אודך בעמים אדני אזמרך בלאמים
10 Gama ƙaunarka mai girma ce, tana kaiwa sammai; amincinka na kaiwa sarari.
כי-גדל עד-שמים חסדך ועד-שחקים אמתך
11 Bari a ɗaukaka ka, ya Allah, bisa sammai; bari ɗaukakarka ta kasance a dukan duniya.
רומה על-שמים אלהים על כל-הארץ כבודך

< Zabura 57 >