< Zabura 55 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil ta Dawuda. Ka ji addu’ata, ya Allah, kada ka ƙyale roƙona;
大衛的訓誨詩,交與伶長。用絲弦的樂器。 上帝啊,求你留心聽我的禱告, 不要隱藏不聽我的懇求!
2 ka ji ni ka kuma amsa mini. Tunanina yana damuna na kuma gaji tilis
求你側耳聽我,應允我。 我哀歎不安,發聲唉哼,
3 hankalina ya tashi saboda yawan surutan masu ƙina, saboda danniyar mugaye. Gama sukan jawo mini wahala, suna jin haushina suna ƙina.
都因仇敵的聲音,惡人的欺壓; 因為他們將罪孽加在我身上,發怒氣逼迫我。
4 Zuciyata tana wahala a cikina; tsorace-tsoracen mutuwa sun sha kaina.
我心在我裏面甚是疼痛; 死的驚惶臨到我身。
5 Tsoro da rawan jiki sun kama ni; razana ta sha kaina.
恐懼戰兢歸到我身; 驚恐漫過了我。
6 Na ce, “Kash, da a ce ina da fikafikan kurciya mana! Ai, da na yi firiya na tafi na huta,
我說:但願我有翅膀像鴿子, 我就飛去,得享安息。
7 da na tafi can da nisa na zauna a hamada; (Sela)
我必遠遊, 宿在曠野。 (細拉)
8 da na hanzarta na tafi wurin mafakata, nesa da muguwar iska da hadiri.”
我必速速逃到避所, 脫離狂風暴雨。
9 Ka rikitar da mugaye, ya Ubangiji, ka birkitar da maganarsu, gama na ga rikici da faɗa a cikin birni.
主啊,求你吞滅他們,變亂他們的舌頭! 因為我在城中見了強暴爭競的事。
10 Dare da rana suna yawo a kan katanga; mugun hali da zargi suna a cikinta.
他們在城牆上晝夜繞行; 在城內也有罪孽和奸惡。
11 Rundunar hallaka suna aiki a cikin birni; barazana da ƙarairayi ba sa taɓa barin titunanta.
邪惡在其中; 欺壓和詭詐不離街市。
12 Da a ce abokin gāba ne ke zagina, da na jure da shi; da a ce maƙiyi yana tā da kansa a kaina, da na ɓoye daga gare shi.
原來不是仇敵辱罵我, 若是仇敵,還可忍耐; 也不是恨我的人向我狂大, 若是恨我的人就必躲避他。
13 Amma kai ne, mutum kamar ni, abokina, abokina na kurkusa,
不料是你;你原與我平等, 是我的同伴,是我知己的朋友!
14 wanda na taɓa jin daɗin zumunci da shi sosai yayinda muke tafiya tare a taron jama’a a gidan Allah.
我們素常彼此談論,以為甘甜; 我們與群眾在上帝的殿中同行。
15 Bari mutuwa ta ɗauki abokan gābana ba labari; bari su gangara da rai zuwa cikin kabari, gama mugunta tana samun masauƙi a cikinsu. (Sheol h7585)
願死亡忽然臨到他們! 願他們活活地下入陰間! 因為他們的住處,他們的心中,都是邪惡。 (Sheol h7585)
16 Amma na kira ga Allah, Ubangiji kuwa ya cece ni.
至於我,我要求告上帝; 耶和華必拯救我。
17 Safe, rana da yamma ina kuka da nishi, yakan kuwa ji muryata.
我要晚上、早晨、晌午哀聲悲歎; 他也必聽我的聲音。
18 Yakan fisshe ni lafiya daga yaƙin da ake yi da ni, ko da yake da yawa suna gāba da ni.
他救贖我命脫離攻擊我的人, 使我得享平安, 因為與我相爭的人甚多。
19 Allah, yana mulki har abada, zai ji su yă kuma azabtar da su, (Sela) mutanen da ba sa taɓa canja hanyoyinsu kuma ba sa tsoron Allah.
那沒有更變、不敬畏上帝的人, 從太古常存的上帝必聽見而苦待他。
20 Abokina ya kai wa abokansa hari; ya tā da alkawarinsa.
他背了約, 伸手攻擊與他和好的人。
21 Maganarsa tana da laushi kamar man zaitun, duk da haka yaƙi yana a cikin zuciyarsa; kalmominsa sun fi mai sulɓi, duk da haka takuba ne zārarru.
他的口如奶油光滑, 他的心卻懷着爭戰; 他的話比油柔和, 其實是拔出來的刀。
22 Ku kawo damuwoyinku ga Ubangiji zai kuwa riƙe ku; ba zai taɓa barin mai adalci yă fāɗi ba.
你要把你的重擔卸給耶和華, 他必撫養你; 他永不叫義人動搖。
23 Amma kai, ya Allah, za ka kawar da mugaye zuwa cikin ramin lalacewa; masu kisa da mutane masu ruɗu ba za su kai rabin kwanakin rayuwarsu ba. Amma ni dai, na dogara gare ka.
上帝啊,你必使惡人下入滅亡的坑; 流人血、行詭詐的人必活不到半世, 但我要倚靠你。

< Zabura 55 >