< Zabura 54 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Zifawa suka tafi wurin Shawulu suka ce, “Ba Dawuda ba ne yake ɓuya a cikinmu?” Ka cece ni, ya Allah ta wurin sunanka; ka nuna ni marar laifi ne ta wurin ƙarfinka.
למנצח בנגינת משכיל לדוד ב בבא הזיפים ויאמרו לשאול הלא דוד מסתתר עמנו ג אלהים בשמך הושיעני ובגבורתך תדינני
2 Ka ji addu’ata, ya Allah; ka saurari maganar bakina.
אלהים שמע תפלתי האזינה לאמרי-פי
3 Baƙi suna kawo mini hari; mutane marasa imani suna neman raina, mutanen da ba sa tsoron Allah. (Sela)
כי זרים קמו עלי-- ועריצים בקשו נפשי לא שמו אלהים לנגדם סלה
4 Tabbatacce Allah ne mai taimakona, Ubangiji shi ne wanda yake riƙe ni.
הנה אלהים עזר לי אדני בסמכי נפשי
5 Bari mugunta ta shaƙe masu magana marar kyau a kaina; cikin amincinka ka hallaka su.
ישוב (ישיב) הרע לשררי באמתך הצמיתם
6 Zan miƙa hadaya ta yardar rai gare ka; zan yabe sunanka, ya Ubangiji, gama yana da kyau.
בנדבה אזבחה-לך אודה שמך יהוה כי-טוב
7 Gama ya cece ni daga dukan wahalolina, idanuna kuma sun ga an yi nasara a kan maƙiyana.
כי מכל-צרה הצילני ובאיבי ראתה עיני

< Zabura 54 >