< Zabura 53 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Bisa ga mahalat. Wani maskil na Dawuda. Wawa ne kawai yakan ce a zuciyarsa, “Ba Allah.” Sun lalace, kuma hanyoyinsu ba su da kyau; babu wani mai aikata abu mai kyau.
למנצח על-מחלת משכיל לדוד ב אמר נבל בלבו אין אלהים השחיתו והתעיבו עול-- אין עשה-טוב
2 Allah yana duba daga sama a kan’ya’yan mutane yă ga ko akwai wani wanda ya gane, wani wanda yake neman Allah.
אלהים-- משמים השקיף על-בני-אדם לראות היש משכיל-- דרש את-אלהים
3 Kowa ya kauce, gaba ɗaya sun lalace; babu guda da yake aikata abu mai kyau, babu ko ɗaya.
כלו סג יחדו נאלחו אין עשה-טוב אין גם-אחד
4 Masu aikata mugunta ba sa taɓa koyo? Suna cin mutanena kamar yadda ake cin burodi, ba sa kuma kira ga Allah.
הלא ידעו פעלי-און אכלי עמי אכלו לחם אלהים לא קראו
5 Ga shi fa, sun firgita don tsoro, ko da yake babu dalilin tsoro, gama Allah zai watsar da ƙasusuwan masu ƙinsa, za su sha kunya, gama Allah ya ƙi su.
שם פחדו פחד-- לא-היה-פחד כי-אלהים--פזר עצמות חנך הבשתה כי-אלהים מאסם
6 Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Allah ya sāke arzuta mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!
מי יתן מציון ישעות ישראל בשוב אלהים שבות עמו יגל יעקב ישמח ישראל

< Zabura 53 >