< Zabura 52 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Wani maskil ta Dawuda. Sa’ad da Doyeg mutumin Edom ya tafi wurin Shawulu ya ce masa, “Dawuda ya tafi gidan Ahimelek.” Me ya sa kake fariya game da mugunta, kai babban mutum? Me ya sa kake fariya dukan yini, kai da kake abin kunya a idanun Allah?
Why boast thou thyself in mischief, O mighty man? The loving kindness of God is continual.
2 Harshenka kan shirya hallaka; yana nan kamar reza mai ci, kana ta ruɗu.
Thy tongue devises wickedness, like a sharp razor, working deceitfully.
3 Kana ƙaunar mugunta fiye da alheri, ƙarya a maimakon faɗin gaskiya. (Sela)
Thou love evil more than good, and lying rather than to speak righteousness. (Selah)
4 Kana ƙaunar kowace kalmar cutarwa, Ya kai harshe mai ruɗu!
Thou love all devouring words, O thou deceitful tongue.
5 Tabbatacce Allah zai kai ka ga madawwamiyar hallaka. Zai fizge ka yă yayyage ka daga tentinka; zai tumɓuke ka daga ƙasar masu rai. (Sela)
God will likewise destroy thee forever. He will take thee up, and pluck thee out of thy tent, and root thee out of the land of the living. (Selah)
6 Masu adalci za su ga su ji tsoro; za su yi masa dariya, suna cewa,
The righteous also shall see, and fear, and shall laugh at him, saying,
7 “Yanzu, ga mutumin da bai mai da Allah mafakarsa ba amma ya dogara a yawan arzikinsa ya kuma yi ƙarfi ta wurin hallaka waɗansu!”
Lo, this is the man who did not make God his strength, but trusted in the abundance of his riches, and strengthened himself in his wickedness.
8 Amma ni kamar itace zaitun ne ina haɓaka a gidan Allah; na dogara ga ƙauna marar ƙarewa ta Allah har abada abadin.
But as for me, I am like a green olive tree in the house of God. I trust in the loving kindness of God forever and ever.
9 Zan yabe ka har abada game da abin da ka yi; a cikin sunanka zan dogara, gama sunanka yana da kyau. Zan yabe ka a gaban tsarkakanka.
I will give thee thanks forever, because thou have done it. And I will hope in thy name in the presence of thy sanctified, for it is good.

< Zabura 52 >