< Zabura 51 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa; bisa ga tausayinka mai girma ka shafe laifofina.
For the leader. A psalm of David, when Nathan the prophet come to him after he had been with Bathsheba. In your kindness, O God, be gracious to me, in your own great pity blot out my transgressions.
2 Ka wanke dukan kurakuraina ka tsarkake ni daga zunubina.
Wash me clean of my guilt, make me pure of my sin.
3 Gama ina sane da laifofina zunubaina kuma kullum suna a gabana.
For well I know my transgressions, my sin is ever before me.
4 Kai kaɗai na yi wa zunubi na yi abin da yake mugu a idonka, ta haka an tabbatar kai mai gaskiya sa’ad da ka yi magana aka kuma nuna kai mai adalci ne sa’ad da ka hukunta.
Against you, only you, have I sinned, and done that which is wrong in your sight: you therefore are just when you speak, and clear when you utter judgment.
5 Tabbatacce ni mai zunubi ne tun haihuwa mai zunubi daga lokacin da mahaifiyata ta yi cikina.
See! In guilt was I brought to the birth, and in sin did my mother conceive me.
6 Tabbatacce kana son gaskiya a sassan ciki; ka koya mini hikima a wuri can ciki.
It’s the innermost truth you desire, give me therefore true wisdom of heart.
7 Ka tsarkake ni da hizzob, zan kuwa zama tsab; ka wanke ni, zan kuma fi dusan ƙanƙara fari.
Purge me clean with hyssop, wash me whiter than snow.
8 Bari in ji farin ciki da murna; bari ƙasusuwan da ka ragargaza su yi farin ciki.
Fill me with joy and gladness, let the bones you have broken rejoice.
9 Ka ɓoye fuskarka daga zunubaina ka kuma shafe dukan kurakuraina.
Hide your face from my sins, and blot out my guilt altogether.
10 Ka halitta zuciya mai tsabta a cikina, ya Allah, ka kuma sabunta tsayayyen ruhu a cikina.
Create me a clean heart, O God, put a new steadfast spirit within me.
11 Kada ka fid da ni daga gabanka ko ka ɗauke Ruhunka Mai Tsarki daga gare ni.
Cast me not forth from your presence, withdraw not your holy spirit.
12 Ka mayar mini farin cikin cetonka ka kuma ba ni ruhun biyayya, yă riƙe ni.
Give me back the joy of your help, with a willing spirit sustain me.
13 Ta haka zan koyar wa masu laifi hanyoyinka, masu zunubi kuma za su komo gare ka.
I will teach your ways to transgressors, and sinners shall turn to you.
14 Ka cece ni daga laifin jini, ya Allah, Allahn da ya cece ni, harshena kuwa zai rera adalcinka.
Save me from blood, O God, and my tongue shall ring out your faithfulness.
15 Ya Ubangiji, ka buɗe leɓunana, bakina kuwa zai furta yabonka.
Open my lips, O Lord, and my mouth shall declare your praise.
16 Ba ka farin ciki a hadaya, ai da na kawo; ba ka jin daɗin hadayun ƙonawa.
For in sacrifice you have no pleasure, in gifts of burnt-offering no delight.
17 Hadayun Allah su ne karyayyen ruhu; karyayyiya da kuma zuciya mai tuba, Ya Allah, ba za ka ƙi ba.
The sacrifice pleasing to God is a spirit that is broken; a heart that is crushed, O God, you will not despise.
18 Cikin jin daɗinka ka sa Sihiyona ta yi nasara; ka gina katangar Urushalima.
Do good in your pleasure to Zion, build the walls of Jerusalem.
19 Ta haka za a kasance da hadayu masu adalci, hadayun ƙonawa ɗungum don su faranta ka; sa’an nan za a miƙa bijimai a bagadenka.
Then will you welcome the due forms of sacrifice, then on your altars shall bullocks be offered.