< Zabura 50 >

1 Zabura ta Asaf. Maɗaukaki, Allah, Ubangiji, ya yi magana ya kuma kira duniya daga fitowar rana zuwa inda take fāɗuwa.
מזמור לאסף אל אלהים יהוה-- דבר ויקרא-ארץ ממזרח-שמש עד-מבאו
2 Daga Sihiyona, cikakkiya a kyau, Allah na haskakawa.
מציון מכלל-יפי-- אלהים הופיע
3 Allahnmu yana zuwa ba kuwa zai yi shiru ba; wuta mai cinyewa a gabansa, babban hadari kuma ya kewaye shi.
יבא אלהינו ואל-יחרש אש-לפניו תאכל וסביביו נשערה מאד
4 Ya kira sammai da suke bisa, da duniya, don yă shari’anta mutanensa.
יקרא אל-השמים מעל ואל-הארץ לדין עמו
5 “Ku tattara mini shafaffuna, waɗanda suka yi alkawari da ni ta wurin hadaya.”
אספו-לי חסידי-- כרתי בריתי עלי-זבח
6 Sammai kuwa sun yi shelar adalcinsa gama Allah kansa alƙali ne. (Sela)
ויגידו שמים צדקו כי-אלהים שפט הוא סלה
7 “Ku ji, ya mutanena, zan kuwa yi magana, Ya Isra’ila, zan kuwa ba da shaida a kanku. Ni ne Allah, Allahnku.
שמעה עמי ואדברה-- ישראל ואעידה בך אלהים אלהיך אנכי
8 Ba na tsawata muku saboda hadayunku ko kuwa hadayunku na ƙonawa, waɗanda kuka taɓa kawo a gabana.
לא על-זבחיך אוכיחך ועולתיך לנגדי תמיד
9 Ba na bukatan bijimi daga turkenku ko awaki daga garkunanku,
לא-אקח מביתך פר ממכלאתיך עתודים
10 gama kowace dabbar kurmi nawa ne, da kuma shanu a kan dubban tuddai.
כי-לי כל-חיתו-יער בהמות בהררי-אלף
11 Na san kowane tsuntsun da yake a duwatsu kuma halittun filaye nawa ne.
ידעתי כל-עוף הרים וזיז שדי עמדי
12 Da a ce ina jin yunwa ai, ba sai na faɗa muku ba, gama duniyar nawa ne, da kome da yake cikinta.
אם-ארעב לא-אמר לך כי-לי תבל ומלאה
13 Ina cin naman bijimai ne ko ina shan jinin awaki ne?
האוכל בשר אבירים ודם עתודים אשתה
14 “Ku miƙa hadayar godiya ga Allah, ku cika alkawuranku ga Mafi Ɗaukaka,
זבח לאלהים תודה ושלם לעליון נדריך
15 ku kira gare ni a ranar wahala; zan cece ku, za ku kuwa girmama ni.”
וקראני ביום צרה אחלצך ותכבדני
16 Amma ga mugaye, Allah ya ce, “Wace dama ce kuke da ita na haddace dokokina ko na yin maganar alkawarina a leɓunanku?
ולרשע אמר אלהים מה-לך לספר חקי ותשא בריתי עלי-פיך
17 Kun ƙi umarnina kuka kuma zubar da kalmomina a bayanku
ואתה שנאת מוסר ותשלך דברי אחריך
18 Sa’ad da kuka ga ɓarawo, kukan haɗa kai da shi; kukan haɗa kai da mazinata.
אם-ראית גנב ותרץ עמו ועם מנאפים חלקך
19 Kuna amfani da bakunanku don mugunta kuna kuma gyara harshenku don ruɗu.
פיך שלחת ברעה ולשונך תצמיד מרמה
20 Kuna ci gaba da magana a kan ɗan’uwanku ku kuma yi maganar ƙarya a kan ɗan mahaifinku.
תשב באחיך תדבר בבן-אמך תתן-דפי
21 Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku.
אלה עשית והחרשתי-- דמית היות-אהיה כמוך אוכיחך ואערכה לעיניך
22 “Ku lura da wannan, ku da kuka manta da Allah, ko kuwa in yayyage ku kucu-kucu, ba kuma wanda zai cece ku.
בינו-נא זאת שכחי אלוה פן-אטרף ואין מציל
23 Shi wanda ya miƙa hadayun godiya yakan girmama ni, ya kuma shirya hanya saboda in nuna masa ceton Allah.”
זבח תודה יכבדנני ושם דרך--אראנו בישע אלהים

< Zabura 50 >