< Zabura 5 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Don Busa. Ta Dawuda. Ka saurare kalmomina, ya Ubangiji, ka ji ajiyar zuciyata.
εἰς τὸ τέλος ὑπὲρ τῆς κληρονομούσης ψαλμὸς τῷ Δαυιδ τὰ ῥήματά μου ἐνώτισαι κύριε σύνες τῆς κραυγῆς μου
2 Ka saurare kukata na neman taimako, Sarkina da Allahna, gama gare ka nake addu’a.
πρόσχες τῇ φωνῇ τῆς δεήσεώς μου ὁ βασιλεύς μου καὶ ὁ θεός μου ὅτι πρὸς σὲ προσεύξομαι κύριε
3 Da safe, ya Ubangiji, ka ji muryata; da safe na gabatar da bukatuna a gabanka in kuma jira da sa zuciya.
τὸ πρωὶ εἰσακούσῃ τῆς φωνῆς μου τὸ πρωὶ παραστήσομαί σοι καὶ ἐπόψομαι
4 Kai ba Allahn da yake jin daɗin mugu ba ne; gama kana gāba da dukan masu aikata mugunta.
ὅτι οὐχὶ θεὸς θέλων ἀνομίαν σὺ εἶ οὐδὲ παροικήσει σοι πονηρευόμενος
5 Masu fariya ba za su iya tsaya a gabanka ba. Kana ƙin duk masu aikata abin da ba daidai ba.
οὐ διαμενοῦσιν παράνομοι κατέναντι τῶν ὀφθαλμῶν σου ἐμίσησας πάντας τοὺς ἐργαζομένους τὴν ἀνομίαν
6 Kakan hallaka masu yin ƙarya. Masu kisankai da mutane masu ruɗu Ubangiji yana ƙyama.
ἀπολεῖς πάντας τοὺς λαλοῦντας τὸ ψεῦδος ἄνδρα αἱμάτων καὶ δόλιον βδελύσσεται κύριος
7 Amma ni, ta wurin jinƙanka mai girma, zan shiga gidanka; da bangirma zan durƙusa ga haikalinka.
ἐγὼ δὲ ἐν τῷ πλήθει τοῦ ἐλέους σου εἰσελεύσομαι εἰς τὸν οἶκόν σου προσκυνήσω πρὸς ναὸν ἅγιόν σου ἐν φόβῳ σου
8 Ka bi da ni, ya Ubangiji, cikin adalcinka saboda abokan gābana, ka fayyace hanyarka a gabana.
κύριε ὁδήγησόν με ἐν τῇ δικαιοσύνῃ σου ἕνεκα τῶν ἐχθρῶν μου κατεύθυνον ἐνώπιόν μου τὴν ὁδόν σου
9 Babu ko kalma guda daga bakinsu da za a dogara da ita; marmarinsu kawai shi ne su hallakar da waɗansu. Maƙogwaronsu buɗaɗɗen kabari ne; da harshensu suna faɗin ƙarya.
ὅτι οὐκ ἔστιν ἐν τῷ στόματι αὐτῶν ἀλήθεια ἡ καρδία αὐτῶν ματαία τάφος ἀνεῳγμένος ὁ λάρυγξ αὐτῶν ταῖς γλώσσαις αὐτῶν ἐδολιοῦσαν
10 Ka furta su masu laifi, ya Allah! Bari makircinsu yă zama fāɗuwarsu. Ka kore su saboda yawan zunubansu, saboda sun tayar maka.
κρῖνον αὐτούς ὁ θεός ἀποπεσάτωσαν ἀπὸ τῶν διαβουλίων αὐτῶν κατὰ τὸ πλῆθος τῶν ἀσεβειῶν αὐτῶν ἔξωσον αὐτούς ὅτι παρεπίκρανάν σε κύριε
11 Amma bari dukan waɗanda suke neman mafaka gare ka su yi murna; bari kullum su yi ta rerawa saboda farin ciki. Ka buɗe kāriyarka a bisansu, domin waɗanda suke ƙaunar sunanka su yi farin ciki a cikinka.
καὶ εὐφρανθήτωσαν πάντες οἱ ἐλπίζοντες ἐπὶ σέ εἰς αἰῶνα ἀγαλλιάσονται καὶ κατασκηνώσεις ἐν αὐτοῖς καὶ καυχήσονται ἐν σοὶ πάντες οἱ ἀγαπῶντες τὸ ὄνομά σου
12 Gama tabbatacce, ya Ubangiji, kakan albarkaci adalai; kakan kewaye su da tagomashinka kamar garkuwa.
ὅτι σὺ εὐλογήσεις δίκαιον κύριε ὡς ὅπλῳ εὐδοκίας ἐστεφάνωσας ἡμᾶς