< Zabura 49 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Na’ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku ji wannan, dukanku mutane; ku saurara, dukanku waɗanda suke zama a wannan duniya,
For the choirmaster. A Psalm of the sons of Korah. Hear this, all you peoples; listen, all inhabitants of the world,
2 babba da yaro mai arziki da talaka.
both low and high, rich and poor alike.
3 Bakina zai yi maganar hikima; magana daga zuciyata za tă ba da ganewa.
My mouth will impart wisdom, and the meditation of my heart will bring understanding.
4 Zan juye kunnena ga karin magana; da garaya zan ƙarfafa kacici-kacicina.
I will incline my ear to a proverb; I will express my riddle with the harp:
5 Don me zan ji tsoro sa’ad da mugayen kwanaki suka zo, sa’ad da mugaye masu ruɗu suka kewaye ni,
Why should I fear in times of trouble, when wicked usurpers surround me?
6 waɗanda suka dogara ga arzikinsu suna kuma fariya a kan yawan arzikinsu?
They trust in their wealth and boast in their great riches.
7 Ba wani da zai iya ceton ran wani ko yă ba wa Allah kuɗin fansa saboda shi,
No man can possibly redeem his brother or pay his ransom to God.
8 kuɗin fansa domin rai yana da tsada, babu abin da za a biya da ya taɓa isa,
For the redemption of his soul is costly, and never can payment suffice,
9 da zai sa yă ci gaba da rayuwa har abada yă hana shi shigan kabari yă ruɓa.
that he should live on forever and not see decay.
10 Gama kowa na iya ganin masu hikima na mutuwa; wawaye da marasa azanci su ma kan hallaka su bar wa waɗansu arzikinsu.
For it is clear that wise men die, and the foolish and the senseless both perish and leave their wealth to others.
11 Kaburburansu za su ci gaba da zama gidajensu har abada, Can za su kasance har zamanai marasa ƙarewa, ko da yake sun ba wa filaye sunayen kansu.
Their graves are their eternal homes— their dwellings for endless generations— even though their lands were their namesakes.
12 Amma mutum, kome arzikinsa, ba ya dawwama; shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
But a man, despite his wealth, cannot endure; he is like the beasts that perish.
13 Wannan ne ƙaddarar waɗanda suke dogara a kansu, da kuma ta mabiyansu, waɗanda suka tabbatar da faɗinsu. (Sela)
This is the fate of the self-confident and their followers who endorse their sayings.
14 Kamar tumaki an ƙaddara su ga kabari; za su kuwa zama abincin mutuwa amma masu gaskiya za su yi mulki a kansu da safe. Kamanninsu za su ruɓe a cikin kabari, nesa da gidajensu masu tsada. (Sheol )
Like sheep they are destined for Sheol. Death will be their shepherd. The upright will rule them in the morning, and their form will decay in Sheol, far from their lofty abode. (Sheol )
15 Amma Allah zai ceci raina daga kabari; tabbatacce zai ɗauke ni zuwa wurinsa. (Sela) (Sheol )
But God will redeem my life from Sheol, for He will surely take me to Himself. (Sheol )
16 Kada ka razana da yawa sa’ad da mutum ya yi arziki sa’ad da darajar gidansa ta ƙaru;
Do not be amazed when a man grows rich, when the splendor of his house increases.
17 gama ba zai ɗauki kome tare da shi sa’ad da ya mutu ba, darajarsa ba za tă gangara tare da shi ba.
For when he dies, he will carry nothing away; his abundance will not follow him down.
18 Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara,
Though in his lifetime he blesses his soul— and men praise you when you prosper—
19 zai gamu da tsarar kakanninsa, waɗanda ba za su taɓa ganin hasken rayuwa ba.
he will join the generation of his fathers, who will never see the light of day.
20 Mutumin da yake da arziki ba tare da ganewa ba shi kamar dabbobi ne da suke mutuwa.
A man who has riches without understanding is like the beasts that perish.