< Zabura 48 >

1 Waƙa ce. Zabura ta’ya’yan Kora maza. Ubangiji mai girma ne, kuma mafificin yabo, a birnin Allahnmu, dutsensa mai tsarki.
שיר מזמור לבני-קרח ב גדול יהוה ומהלל מאד-- בעיר אלהינו הר-קדשו
2 Kyakkyawa ce cikin tsayinta, abin farin cikin dukan duniya. Kamar ƙwanƙoli mafi tsayi na Zafon ne Dutsen Sihiyona, birnin Babban Sarki.
יפה נוף משוש כל-הארץ הר-ציון ירכתי צפון קרית מלך רב
3 Allah yana cikin fadodinta; ya nuna kansa mafaka ce gare ta.
אלהים בארמנותיה נודע למשגב
4 Sa’ad da sarakuna suka haɗa rundunoni, sa’ad da suka yi gaba tare,
כי-הנה המלכים נועדו עברו יחדו
5 sun gan ta suka kuwa yi mamaki; suka gudu don tsoro.
המה ראו כן תמהו נבהלו נחפזו
6 Rawar jiki ya kama su a can, zafi kamar na mace mai naƙuda.
רעדה אחזתם שם חיל כיולדה
7 Ka hallaka su kamar jiragen ruwan Tarshish da iskar gabas ta wargaje.
ברוח קדים-- תשבר אניות תרשיש
8 Yadda muka ji, haka muka gani a cikin birnin Ubangiji Maɗaukaki, a cikin birnin Allahnmu. Allah ya sa ta zauna lafiya har abada. (Sela)
כאשר שמענו כן ראינו-- בעיר-יהוה צבאות בעיר אלהינו אלהים יכוננה עד-עולם סלה
9 Cikin haikalinka, ya Allah, mun yi tunani a kan ƙaunarka marar ƙarewa.
דמינו אלהים חסדך-- בקרב היכלך
10 Kamar sunanka, ya Allah, yabonka ya kai iyakokin duniya; hannunka na dama ya cika da adalci.
כשמך אלהים-- כן תהלתך על-קצוי-ארץ צדק מלאה ימינך
11 Dutsen Sihiyona ya yi farin ciki, ƙauyukan Yahuda suna murna saboda hukuntanka.
ישמח הר ציון--תגלנה בנות יהודה למען משפטיך
12 Yi tafiya cikin Sihiyona, ku kewaye ta, ku ƙirga hasumiyoyinta,
סבו ציון והקיפוה ספרו מגדליה
13 ku lura da katangarta da kyau, ku dubi fadodinta, don ku faɗe su ga tsara mai zuwa.
שיתו לבכם לחילה--פסגו ארמנותיה למען תספרו לדור אחרון
14 Gama wannan Allah shi ne Allahnmu har abada abadin; zai zama jagorarmu har zuwa ƙarshe.
כי זה אלהים אלהינו--עולם ועד הוא ינהגנו על-מות

< Zabura 48 >