< Zabura 47 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta’Ya’yan Kora maza. Zabura ce. Ku tafa hannuwanku, dukanku al’ummai; ku yi sowa ga Allah da muryoyin farin ciki.
For the leader. Of the Korahites. A psalm. Clap your hands, all you peoples: shout to God in ringing cries.
2 Ubangiji Mafi Ɗaukaka mai banmamaki ne, Sarki ne mai girma a bisa dukan duniya!
For the Lord is most high and dread, a great king over all the earth.
3 Ya rinjayi al’ummai a ƙarƙashinmu, mutane kuma a ƙarƙashin ƙafafunmu.
He subdues the peoples under us, the nations under our feet;
4 Ya zaɓar mana gādonmu, abar taƙamar Yaƙub, wanda yake ƙauna. (Sela)
he chooses our heritage for us, the glory of Jacob whom he loves. (Selah)
5 Allah ya haura a cikin sowa ta farin ciki, Ubangiji ya haura a cikin ƙarar ƙahoni.
God is gone up with a shout, the Lord with the sound of a trumpet.
6 Ku rera yabai ga Allah, ku rera yabai; ku rera yabai ga Sarkinmu, ku rera yabai.
Sing praise to our God, sing praises: sing praise to our king, sing praises.
7 Gama Allah shi ne Sarkin dukan duniya; ku rera zabura ta yabo gare shi.
For king of all earth is he: praise God in a skilful song.
8 Allah yana mulki a bisa al’ummai; Allah yana zama a kan kursiyinsa mai tsarki.
God is king over all the nations, God sits on his holy throne.
9 Manyan mutanen al’ummai sun taru a matsayin mutanen Allah na Ibrahim, gama sarkunan duniya na Allah ne; ana ɗaukaka shi ƙwarai.
Princes of nations gather with the people of Abraham’s God: for the shields of the earth are God’s; greatly exalted is he.

< Zabura 47 >