< Zabura 46 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta’Ya’yan Kora maza. Bisa ga alamot Waƙa ce. Allah ne mafakarmu da ƙarfinmu, kullum yana a shirye yă taimaka a lokacin wahala.
2 Saboda haka ba za mu ji tsoro ba, ko da ƙasa ta girgiza duwatsu kuma suka fāɗi cikin zurfin teku,
3 ko da ruwansa suna ruri suna kumfa duwatsu kuma suna girgiza da tumbatsansu. (Sela)
4 Akwai kogi mai rafuffukan da suke sa birnin Allah murna, tsattsarkan wuri inda Mafi Ɗaukaka ke zama.
5 Allah yana cikinta, ba za tă fāɗi ba; Allah zai taimake ta da safe.
6 Al’ummai suna hayaniya, mulkoki sun fāɗi; ya ɗaga muryarsa, duniya ta narke.
7 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. (Sela)
8 Zo ku ga ayyukan Ubangiji, kangon da ya kawo a kan duniya.
9 Ya sa yaƙoƙi suka yi tsit ko’ina a duniya. Ya kakkarya bakkuna ya kuma ragargaza māsu, ya ƙone garkuwoyi da wuta.
10 “Ku natsu ku kuma san cewa ni ne Allah; za a ɗaukaka ni a cikin al’ummai, za a ɗaukaka ni cikin duniya.”
11 Ubangiji Maɗaukaki yana tare da mu; Allah na Yaƙub ne kagararmu. (Sela)