< Zabura 45 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Lili.” Na’ya’yan Kora maza. Maskil Waƙar Aure. Zuciyata ta cika da kyakkyawan kan magana yayinda nake rera ayoyina wa sarki; harshena ne alƙalamin ƙwararren marubuci.
For the leader; on shoshannim. Of the Korahites. A maskil. A love song. My heart is astir with beautiful words: I will sing a song, concerning the king, with tongue like the pen of a ready writer.
2 Kai ne mafi kyau cikin mutane an kuma shafe leɓunanka da alheri, da yake Allah ya albarkace ka har abada.
Your beauty is more than mortal, grace is shed over your lips: therefore God has blessed you forever.
3 Ka ɗaura takobinka a gefenka, ya jarumi; ka rufe kanka da ɗaukaka da kuma daraja.
Warrior, strap your sword on your thigh. What glory and splendor!
4 Cikin darajarka ka hau zuwa nasara a madadin gaskiya, tawali’u da adalci; bari hannunka na dama yă nuna ayyukan banmamaki.
Good fortune attend you, as forth you ride in the cause of good faith, and as champion of justice. May your arm instruct you in deeds of dread.
5 Bari kibiyoyinka masu tsini su huda zukatan abokan gāban sarki; bari al’ummai su fāɗi ƙarƙashin ƙafafunka.
Sharp are your arrows; nations fall under you: pierced to the heart are the foes of the king.
6 Kursiyinka, ya Allah, zai kasance har abada abadin; sandar adalci zai zama sandar mulkinka.
Your throne shall endure for ever and ever your royal sceptre a sceptre of equity.
7 Kana ƙaunar abin da yake daidai kana kuma ƙin mugunta; saboda haka Allah, Allahnka, ya sa ka a bisa abokanka ta wurin shafe ka da man farin ciki.
Right you love and wrong you hate: therefore the Lord your God anoints you With oil of gladness above your fellows.
8 Dukan rigunanka suna ƙanshin turaren mur da na aloyes, da na kashiya; daga kowace fadan da aka yi masa ado da hauren giwa kaɗe-kaɗen tsirkiya kan sa ka murna.
With myrrh, aloes, and cassia your robes are all fragrant, you are gladdened by music of ivory harps.
9 ’Ya’yan sarki mata suna cikin matan da ake girmama; a hannun damarka kuwa ga amarya, sarauniya saye da ofir zinariya.
King’s daughters stand ready with jewels for you, at your right hand the queen in gold of Ophir.
10 Ki saurara, ya ke diya, ki lura ku kuma kasa kunne, Ki manta da mutanenki da gidan mahaifinki.
Listen, daughter, and see; and incline your ear: forget your folk and your father’s house.
11 Sarki ya cika da sha’awar kyanki; ki girmama shi, gama shi ne maigidanki.
And when the king desires your beauty, bow to him, for he is your lord.
12 Diyar Taya za tă zo da kyauta, mawadata za su nemi tagomashinki.
So shall the Tyrians come with gifts, and the richest of people will do you homage.
13 Gimbiya tana fada, kyakkyawa ce ainun; an saƙa rigarta da zaren zinariya.
The king’s daughter is glorious altogether, with dress of pearls inwrought with gold.
14 Cikin riguna masu ado aka kai ta wurin sarki; abokanta budurwai suna biye da ita aka kuwa kawo su gare ka.
In many-coloured robes she is led to the king, with the virgin companions she brought in her train.
15 Aka bi da su cikin farin ciki da murna; suka shiga fadan sarki.
The king’s palace they enter with joy and rejoicing.
16 ’Ya’yanka maza za su maye matsayin kakanninka; za ka sa su yi mulki a duk fāɗin ƙasar.
May sons of yours take the place of your fathers, whom you will make princes in all the land.
17 Zan sa a tuna da kai a dukan zamanai; saboda haka al’ummai za su yabe ka har abada abadin.
Your name will I celebrate world without end, so that nations shall praise you for ever and ever.

< Zabura 45 >