< Zabura 44 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta’ya’yan Kora maza. Maskil ne. Mun ji da kunnuwanmu, ya Allah; kakanninmu sun faɗa mana abin da ka aikata a kwanakinsu, tun dā can.
For the choirmaster. A Maskil of the sons of Korah. We have heard with our ears, O God; our fathers have told us the work You did in their days, in the days of old.
2 Da hannunka ka kori al’ummai ka kuma dasa kakanninmu; ka ragargaza mutanen ka kuma sa kakanninmu suka haɓaka.
With Your hand You drove out the nations and planted our fathers there; You crushed the peoples and cast them out.
3 Ba da takobinsu ba ne suka ci ƙasar, ba kuwa ƙarfin hannunsu ne ya ba su nasara ba; hannun damanka ne, ƙarfin hannunka, da kuma hasken fuskarka, gama ka ƙaunace su.
For it was not by their sword that they took the land; their arm did not bring them victory. It was by Your right hand, Your arm, and the light of Your face, because You favored them.
4 Kai ne Sarkina da kuma Allahna, wanda ya ba da nasarori wa Yaƙub.
You are my King, O God, who ordains victories for Jacob.
5 Ta wurinka mun tura abokan gābanmu baya; ta wurin sunanka muka tattake maƙiyanmu.
Through You we repel our foes; through Your name we trample our enemies.
6 Ba na dogara ga bakana, takobina ba ya kawo nasara;
For I do not trust in my bow, nor does my sword save me.
7 amma kana ba mu nasara a kan abokan gābanmu, ka sa abokan gābanmu suka sha kunya.
For You save us from our enemies; You put those who hate us to shame.
8 A cikin Allah muke fariyarmu dukan yini, kuma za mu yabi sunanka har abada. (Sela)
In God we have boasted all day long, and Your name we will praise forever.
9 Amma yanzu ka ƙi mu ka kuma ƙasƙantar da mu; ba ka ƙara fita tare da mayaƙanmu.
But You have rejected and humbled us; You no longer go forth with our armies.
10 Ka sa muka gudu a gaban abokin gāba, kuma abokan gābanmu suka washe mu.
You have made us retreat from the foe, and those who hate us have plundered us.
11 Ka ba da mu a cinye kamar tumaki ka kuma watsar da mu a cikin al’ummai.
You have given us up as sheep to be devoured; You have scattered us among the nations.
12 Ka sayar da mutanenka a kuɗin da bai taka ƙara ya karye ba babu wata riba daga sayar da su da ka yi.
You sell Your people for nothing; no profit do You gain from their sale.
13 Ka mai da mu abin dariya ga maƙwabtanmu, abin dariya da reni ga waɗanda suke kewaye da mu.
You have made us a reproach to our neighbors, a mockery and derision to those around us.
14 Ka sa muka zama abin ba’a a cikin al’ummai; mutanen suna kaɗa mana kai.
You have made us a byword among the nations, a laughingstock among the peoples.
15 Dukan yini ina cikin wulaƙanci, fuskata kuma ta rufu da kunya
All day long my disgrace is before me, and shame has covered my face,
16 saboda ba’ar waɗanda suke zagi suke kuma ƙina, saboda abokan gābana, waɗanda suka sha alwashi sai sun yi ramuwa.
at the voice of the scorner and reviler, because of the enemy, bent on revenge.
17 Dukan wannan ya faru da mu, ko da yake ba mu manta da kai ba ko mu kasance masu ƙarya ga alkawarinka.
All this has come upon us, though we have not forgotten You or betrayed Your covenant.
18 Zukatanmu ba su juya baya; ƙafafunmu ba su kauce daga hanyarka ba.
Our hearts have not turned back; our steps have not strayed from Your path.
19 Amma ka ragargaza mu ka kuma maishe mu abin farautar karnukan jeji ka kuma rufe mu cikin duhu baƙi ƙirin.
But You have crushed us in the lair of jackals; You have covered us with deepest darkness.
20 Da a ce mun manta da sunan Allahnmu ko mun miƙa hannuwanmu ga baƙin alloli,
If we had forgotten the name of our God or spread out our hands to a foreign god,
21 da Allah bai gane ba, da yake ya san asiran zuciya?
would not God have discovered, since He knows the secrets of the heart?
22 Duk da haka saboda kai mun fuskanci mutuwa dukan yini; aka ɗauke mu kamar tumakin da za a yanka.
Yet for Your sake we face death all day long; we are considered as sheep to be slaughtered.
23 Ka farka, ya Ubangiji! Don me kake barci? Ta da kanka! Kada ka ƙi mu har abada.
Wake up, O Lord! Why are You sleeping? Arise! Do not reject us forever.
24 Me ya sa ka ɓoye fuskarka ka manta da azabanmu da kuma danniyar da ake mana?
Why do You hide Your face and forget our affliction and oppression?
25 An kai mu ƙasa zuwa ƙura; jikunanmu sun manne da ƙasa.
For our soul has sunk to the dust; our bodies cling to the earth.
26 Ka tashi ka taimake mu; ka cece mu saboda ƙaunarka marar ƙarewa.
Rise up; be our help! Redeem us on account of Your loving devotion.