< Zabura 41 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Mai albarka ne wanda yake jin tausayin marasa ƙarfi; Ubangiji yakan kuɓutar da shi a lokutan wahala.
למנצח מזמור לדוד אשרי משכיל אל דל ביום רעה ימלטהו יהוה׃
2 Ubangiji zai kāre shi yă kuma kiyaye ransa; zai albarkace shi a cikin ƙasar ba kuwa zai miƙa shi ga hannun maƙiyansa ba.
יהוה ישמרהו ויחיהו יאשר בארץ ואל תתנהו בנפש איביו׃
3 Ubangiji zai ba shi ƙarfi a gadon rashin lafiyarsa ya mayar masa da lafiya daga ciwon da ya kwantar da shi.
יהוה יסעדנו על ערש דוי כל משכבו הפכת בחליו׃
4 Na ce, “Ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai; ka warkar da ni, gama na yi maka zunubi.”
אני אמרתי יהוה חנני רפאה נפשי כי חטאתי לך׃
5 Abokan gābana suna muguwar magana a kaina cewa, “Yaushe zai mutu sunansa yă ɓace ne?”
אויבי יאמרו רע לי מתי ימות ואבד שמו׃
6 Duk sa’ad da wani ya zo ganina, yakan yi maganar ƙarya, yayinda zuciyarsa tana tattare da cin zarafi; sa’an nan yă fita yă yi ta bazawa ko’ina.
ואם בא לראות שוא ידבר לבו יקבץ און לו יצא לחוץ ידבר׃
7 Dukan abokan gābana suna raɗa tare a kaina; suna fata mugun abu ya same ni, suna cewa,
יחד עלי יתלחשו כל שנאי עלי יחשבו רעה לי׃
8 “Mugun ciwo ya kama shi; ba zai taɓa tashi daga inda yake kwanciya ba.”
דבר בליעל יצוק בו ואשר שכב לא יוסיף לקום׃
9 Har abokina na kurkusa, wanda na amince da shi, wanda muke cin abinci tare, ya juya yana gāba da ni.
גם איש שלומי אשר בטחתי בו אוכל לחמי הגדיל עלי עקב׃
10 Amma kai, ya Ubangiji, ka yi mini jinƙai, ka tā da ni, don in sāka musu.
ואתה יהוה חנני והקימני ואשלמה להם׃
11 Na sani kana jin daɗina, gama abokin gābana ba zai ci nasara a kaina ba.
בזאת ידעתי כי חפצת בי כי לא יריע איבי עלי׃
12 Cikin mutuncina ka riƙe ni ka sa ni a gabanka har abada.
ואני בתמי תמכת בי ותציבני לפניך לעולם׃
13 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, Allah na Isra’ila, har abada abadin.
ברוך יהוה אלהי ישראל מהעולם ועד העולם אמן ואמן׃

< Zabura 41 >