< Zabura 40 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Na jira da haƙuri ga Ubangiji; ya juya wurina ya kuma ji kukata.
למנצח לדוד מזמור קוה קויתי יהוה ויט אלי וישמע שועתי׃
2 Ya ɗaga ni daga rami marar fāɗi, daga laka da taɓo; ya sa ƙafafuna a kan dutse ya kuma ba ni tsayayyen wuri don in tsaya.
ויעלני מבור שאון מטיט היון ויקם על סלע רגלי כונן אשרי׃
3 Ya sa sabuwar waƙa a bakina, waƙar yabo ga Allahna. Da yawa za su gani su tsorata su kuma dogara ga Ubangiji.
ויתן בפי שיר חדש תהלה לאלהינו יראו רבים וייראו ויבטחו ביהוה׃
4 Mai albarka ne mutumin da ya mai da Ubangiji abin dogararsa, wanda ba ya kula da masu girman kai, waɗanda suka juya ga allolin ƙarya.
אשרי הגבר אשר שם יהוה מבטחו ולא פנה אל רהבים ושטי כזב׃
5 Da yawa ne, ya Ubangiji Allahna, abubuwan banmamakin da ka aikata. Abubuwan da ka shirya mana. Ba wanda zai iya faɗa maka su; a ce zan yi magana in faɗe su, za su wuce gaban misali a furta.
רבות עשית אתה יהוה אלהי נפלאתיך ומחשבתיך אלינו אין ערך אליך אגידה ואדברה עצמו מספר׃
6 Hadaya da sadaka ba ka sha’awa, amma kunnuwana ka huda; hadayun ƙonawa da hadayun zunubi ba ka bukata.
זבח ומנחה לא חפצת אזנים כרית לי עולה וחטאה לא שאלת׃
7 Sa’an nan na ce, “Ga ni, na zo, kamar yadda yake a rubuce game da ni cikin littafi.
אז אמרתי הנה באתי במגלת ספר כתוב עלי׃
8 Ina sha’awar aikata nufinka, ya Allahna; dokar tana cikin zuciyata.”
לעשות רצונך אלהי חפצתי ותורתך בתוך מעי׃
9 Na yi shelar adalcinka cikin babban taro; ba na rufe leɓunana, kamar yadda ka sani, ya Ubangiji.
בשרתי צדק בקהל רב הנה שפתי לא אכלא יהוה אתה ידעת׃
10 Ba na ɓoye adalcinka cikin zuciyata; ina maganar amincinka da cetonka. Ban ɓoye ƙaunarka da gaskiyarka a gaban taron jama’arka mai girma ba.
צדקתך לא כסיתי בתוך לבי אמונתך ותשועתך אמרתי לא כחדתי חסדך ואמתך לקהל רב׃
11 Kada ka hana mini jinƙanka, ya Ubangiji; bari ƙaunarka da gaskiyarka kullum su kāre ni.
אתה יהוה לא תכלא רחמיך ממני חסדך ואמתך תמיד יצרוני׃
12 Gama damuwoyin da suka wuce misali sun kewaye ni; zunubaina sun mamaye ni, kuma ba na iya gani. Sun fi gashin kaina yawa, har ma na fid da zuciya.
כי אפפו עלי רעות עד אין מספר השיגוני עונתי ולא יכלתי לראות עצמו משערות ראשי ולבי עזבני׃
13 Ka ji daɗin cetona, ya Ubangiji; Ya Ubangiji, ka zo da sauri ka taimake ni.
רצה יהוה להצילני יהוה לעזרתי חושה׃
14 Bari masu neman raina su sha kunya su kuma rikice; bari dukan waɗanda suke neman lalacewata su koma baya da kunya.
יבשו ויחפרו יחד מבקשי נפשי לספותה יסגו אחור ויכלמו חפצי רעתי׃
15 Bari masu ce mini, “Allah yă ƙara!” Su sha mamaki saboda kunyar da za su sha.
ישמו על עקב בשתם האמרים לי האח האח׃
16 Amma bari dukan masu nemanka su yi farin ciki su kuma yi murna a cikinka; bari waɗanda suke ƙaunar cetonka kullum su ce, “Ubangiji mai girma ne!”
ישישו וישמחו בך כל מבקשיך יאמרו תמיד יגדל יהוה אהבי תשועתך׃
17 Ni dai matalauci ne da mai bukata; bari Ubangiji yă tuna da ni. Kai ne taimakona da mai cetona; Ya Allahna, kada ka jinkirta.
ואני עני ואביון אדני יחשב לי עזרתי ומפלטי אתה אלהי אל תאחר׃

< Zabura 40 >