< Zabura 38 >

1 Zabura ta Dawuda. Roƙo ne. Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka.
מזמור לדוד להזכיר יהוה אל בקצפך תוכיחני ובחמתך תיסרני׃
2 Gama kibiyoyinka sun soke ni, hannunka kuma ya fāɗo a kaina.
כי חציך נחתו בי ותנחת עלי ידך׃
3 Saboda hasalarka babu lafiya a jikina; ƙasusuwana ba lafiya saboda zunubina.
אין מתם בבשרי מפני זעמך אין שלום בעצמי מפני חטאתי׃
4 Laifofina sun mamaye ni kamar nauyin da ya sha ƙarfin ɗauka.
כי עונתי עברו ראשי כמשא כבד יכבדו ממני׃
5 Miyakuna sun ruɓe suna kuma wari saboda wawancina na zunubi.
הבאישו נמקו חבורתי מפני אולתי׃
6 An tanƙware ni aka kuma ƙasƙantar da ni; dukan yini ina ta kuka.
נעויתי שחתי עד מאד כל היום קדר הלכתי׃
7 Bayana yana fama da zazzaɓi; babu lafiya a jikina.
כי כסלי מלאו נקלה ואין מתם בבשרי׃
8 Na gaji sharkaf an kuma ragargaza ni; ina nishi da wahala a cikin zuciyata.
נפוגותי ונדכיתי עד מאד שאגתי מנהמת לבי׃
9 Dukan bukatata tana a shimfiɗe a gabanka, ya Ubangiji; ajiyar zuciyata ba ta ɓoyuwa daga gare ka.
אדני נגדך כל תאותי ואנחתי ממך לא נסתרה׃
10 Zuciyata na bugu, ƙarfina kuma ya ƙare, har ma haske ya rabu da idanuna.
לבי סחרחר עזבני כחי ואור עיני גם הם אין אתי׃
11 Abokaina da maƙwabtana sun guje ni saboda miyakuna; maƙwabtana ba sa zuwa kusa.
אהבי ורעי מנגד נגעי יעמדו וקרובי מרחק עמדו׃
12 Waɗanda suke neman raina sun sa tarkonsu, waɗanda suke so su cuce ni suna zance lalatar da ni; yini sukutum suna ƙulla mini maƙarƙashiya.
וינקשו מבקשי נפשי ודרשי רעתי דברו הוות ומרמות כל היום יהגו׃
13 Ni kamar kurma ne, wanda ba ya ji, kamar bebe, wanda ba ya iya buɗe bakinsa.
ואני כחרש לא אשמע וכאלם לא יפתח פיו׃
14 Na zama kamar mutumin da ba ya ji, wanda bakinsa ba ya iya ba da amsa.
ואהי כאיש אשר לא שמע ואין בפיו תוכחות׃
15 Na dogara gare ka, ya Ubangiji; za ka amsa, ya Ubangiji Allahna.
כי לך יהוה הוחלתי אתה תענה אדני אלהי׃
16 Gama na ce, “Kada ka bar su su yi farin ciki a kaina ko su yi kirari a kaina sa’ad da ƙafata ta yi santsi.”
כי אמרתי פן ישמחו לי במוט רגלי עלי הגדילו׃
17 Gama ina gab da fāɗuwa, kuma cikin azaba nake kullum.
כי אני לצלע נכון ומכאובי נגדי תמיד׃
18 Na furta laifina; na damu da zunubina.
כי עוני אגיד אדאג מחטאתי׃
19 Da yawa ne masu gāba da ni da ƙarfi; waɗanda suke kina ba dalili sun yi yawa.
ואיבי חיים עצמו ורבו שנאי שקר׃
20 Waɗanda suke sāka alherina da mugunta, suna cin zarafina sa’ad da nake bin abin da yake daidai.
ומשלמי רעה תחת טובה ישטנוני תחת רדופי טוב׃
21 Ya Ubangiji, kada ka yashe ni; kada ka yi nesa da ni, ya Allahna.
אל תעזבני יהוה אלהי אל תרחק ממני׃
22 Zo da sauri ka taimake ni, Ya Ubangiji Mai Cetona.
חושה לעזרתי אדני תשועתי׃

< Zabura 38 >