< Zabura 37 >

1 Ta Dawuda. Kada ka tsorata saboda mugayen mutane ko ka yi kishin waɗanda suka aikata mugunta;
לדוד אל-תתחר במרעים אל-תקנא בעשי עולה
2 gama kamar ciyawa za su bushe, kamar ɗanyun ganyaye za su mutu.
כי כחציר מהרה ימלו וכירק דשא יבולון
3 Ka dogara ga Ubangiji ka kuma aikata alheri; yi zama cikin ƙasar ka kuma more makiyaya mai lafiya.
בטח ביהוה ועשה-טוב שכן-ארץ ורעה אמונה
4 Ka ji daɗinka a cikin Ubangiji zai kuwa biya bukatun zuciyarka.
והתענג על-יהוה ויתן-לך משאלת לבך
5 Ka sa kanka a hanyar Ubangiji; ka kuma dogara gare shi zai kuwa yi wannan.
גול על-יהוה דרכך ובטח עליו והוא יעשה
6 Zai sa adalcinka yă haskaka kamar hasken safiya, gaskiyarka kuma kamar rana a tsaka.
והוציא כאור צדקך ומשפטך כצהרים
7 Ka natsu a gaban Ubangiji ka kuma jira da haƙuri gare shi; kada ka tsorata sa’ad da mutane ke nasara a hanyoyinsu, sa’ad da suke aikata mugayen shirye-shiryensu.
דום ליהוה-- והתחולל-לו אל-תתחר במצליח דרכו באיש עשה מזמות
8 Kada ka yi fushi kada kuma ka yi hasala; kada ka tsorata, wannan yakan kai ga mugunta ne kawai.
הרף מאף ועזב חמה אל-תתחר אך-להרע
9 Gama za a datse mugayen mutane, amma waɗanda suke sa zuciya ga Ubangiji za su gāji ƙasar.
כי-מרעים יכרתון וקוי יהוה המה יירשו-ארץ
10 A ɗan ƙanƙanen lokaci, mugaye za su shuɗe; ko ka neme su, ba za a same su ba.
ועוד מעט ואין רשע והתבוננת על-מקומו ואיננו
11 Amma masu tawali’u za su gāji ƙasar su kuma zauna da cikakkiyar salama.
וענוים יירשו-ארץ והתענגו על-רב שלום
12 Mugaye sukan shirya wa adalai maƙarƙashiya su ciji baki a kansu;
זמם רשע לצדיק וחרק עליו שניו
13 amma Ubangiji yakan yi dariyar mugaye, gama ya sani ranarsu tana zuwa.
אדני ישחק-לו כי-ראה כי-יבא יומו
14 Mugaye sukan zare takobi su ja baka don su kashe matalauta da masu bukata, don su kashe waɗanda hanyoyinsu daidai suke.
חרב פתחו רשעים-- ודרכו קשתם להפיל עני ואביון לטבוח ישרי-דרך
15 Amma takubansu za su soki zukatansu, kuma bakkunansu za su kakkarye.
חרבם תבוא בלבם וקשתותם תשברנה
16 Ƙanƙanen abin da mai adalci yake da shi ya fi arzikin mugaye yawa;
טוב-מעט לצדיק-- מהמון רשעים רבים
17 gama za a kakkarya ikon mugaye, amma Ubangiji zai riƙe mai adalci.
כי זרועות רשעים תשברנה וסומך צדיקים יהוה
18 Kwanakin marasa zarge suna sane ga Ubangiji, kuma gādonsu zai dawwama har abada.
יודע יהוה ימי תמימם ונחלתם לעולם תהיה
19 A lokutan masifu ba za su yanƙwane ba; a kwanakin yunwa za su sami a yalwace.
לא-יבשו בעת רעה ובימי רעבון ישבעו
20 Amma mugaye za su hallaka, Abokan gāban Ubangiji za su zama kamar kyan gonaki, za su ɓace, za su ɓace kamar hayaƙi.
כי רשעים יאבדו ואיבי יהוה כיקר כרים כלו בעשן כלו
21 Mugaye kan yi rance ba sa kuma biya, amma masu adalci suna bayar hannu sake;
לוה רשע ולא ישלם וצדיק חונן ונותן
22 waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka za su gāji ƙasar, amma waɗanda ya la’anta, za a kore su.
כי מברכיו יירשו ארץ ומקלליו יכרתו
23 In Ubangiji ya ji daɗin hanyar da mutum yake bi, zai sa sawu su kahu;
מיהוה מצעדי-גבר כוננו ודרכו יחפץ
24 ko ya yi tuntuɓe, ba zai fāɗi ba, gama Ubangiji yakan riƙe shi da hannunsa.
כי-יפל לא-יוטל כי-יהוה סומך ידו
25 Dā ni yaro ne amma yanzu na tsufa, duk da haka ban taɓa ganin an yashe masu adalci ba ko a ce’ya’yansu suna roƙon burodi.
נער הייתי-- גם-זקנתי ולא-ראיתי צדיק נעזב וזרעו מבקש-לחם
26 Kullum suna bayar hannu sake suna kuma ba da bashi ba da wahala ba, za a yi wa’ya’yansu albarka.
כל-היום חונן ומלוה וזרעו לברכה
27 Ku juyo daga mugunta ku yi alheri; sa’an nan za ku zauna a ƙasar har abada.
סור מרע ועשה-טוב ושכן לעולם
28 Gama Ubangiji yana ƙaunar masu aikata daidai kuma ba zai yashe amintattunsa ba. Za a hallaka masu aikata mugunta gaba ɗaya,’ya’yan mugaye za su hallaka.
כי יהוה אהב משפט ולא-יעזב את-חסידיו לעולם נשמרו וזרע רשעים נכרת
29 Masu adalci za su gāji ƙasar su kuma zauna a cikinta har abada.
צדיקים יירשו-ארץ וישכנו לעד עליה
30 Bakin mutum mai adalci yakan yi magana da hikima, harshensa kuwa yakan yi maganar abin da yake daidai.
פי-צדיק יהגה חכמה ולשונו תדבר משפט
31 Dokar Allahnsa tana a cikin zuciyarsa; ƙafafunsa ba sa santsi.
תורת אלהיו בלבו לא תמעד אשריו
32 Mugaye suna fako suna jira masu adalci, suna ƙoƙari neman ransu;
צופה רשע לצדיק ומבקש להמיתו
33 amma Ubangiji ba zai bar su a ikonsu ba ko ya bari a hukunta su sa’ad da aka kawo su shari’a ba.
יהוה לא-יעזבנו בידו ולא ירשיענו בהשפטו
34 Ku sa zuciya ga Ubangiji ku kuma kiyaye hanyarsa. Zai ɗaukaka ku ku ci gādon ƙasar, sa’ad da aka kawar da mugaye, za ka gani.
קוה אל-יהוה ושמר דרכו וירוממך לרשת ארץ בהכרת רשעים תראה
35 Na ga wani mugu, azzalumi, yana yaɗuwa kamar ɗanyen itace a asalin ƙasarsa,
ראיתי רשע עריץ ומתערה כאזרח רענן
36 amma yakan mutu nan da nan kuma ba ya ƙara kasancewa; ko an neme shi, ba za a same shi ba.
ויעבר והנה איננו ואבקשהו ולא נמצא
37 Ka dubi marasa zargi, ka lura da adali; akwai sa zuciya domin mutum mai salama.
שמר-תם וראה ישר כי-אחרית לאיש שלום
38 Amma za a hallaka dukan masu zunubi; za a yanke sa zuciya ta mugaye.
ופשעים נשמדו יחדו אחרית רשעים נכרתה
39 Ceton adalai kan zo daga Ubangiji; shi ne mafaka a lokacin wahala.
ותשועת צדיקים מיהוה מעוזם בעת צרה
40 Ubangiji yakan taimake su yă kuma cece su; yakan kuɓutar da su daga mugaye yă kuma cece su, domin sukan nemi mafaka daga gare shi.
ויעזרם יהוה ויפלטם יפלטם מרשעים ויושיעם--כי-חסו בו

< Zabura 37 >