< Zabura 35 >

1 Ta Dawuda. Yi hamayya, ya Ubangiji, da waɗanda suke hamayya da ni; yi faɗa da waɗanda suke faɗa da ni.
לְדָוִד ׀ רִיבָה יְהוָה אֶת־יְרִיבַי לְחַם אֶת־לֹֽחֲמָֽי׃
2 Ka ɗauki garkuwa da kuma makami; ka tashi ka taimake ni.
הַחֲזֵק מָגֵן וְצִנָּה וְקוּמָה בְּעֶזְרָתִֽי׃
3 Ka ɗaga māshi da kuma abin da ake jefa a kan waɗanda suke fafarata. Ka ce wa raina, “Ni ne cetonka.”
וְהָרֵק חֲנִית וּסְגֹר לִקְרַאת רֹדְפָי אֱמֹר לְנַפְשִׁי יְֽשֻׁעָתֵךְ אָֽנִי׃
4 Bari waɗanda suke neman raina su sha kunya a kuma kunyatar da su; bari waɗanda suke shirya lalacewata su juya da baya su ruɗe.
יֵבֹשׁוּ וְיִכָּלְמוּ מְבַקְשֵׁי נַפְשִׁי יִסֹּגוּ אָחוֹר וְיַחְפְּרוּ חֹשְׁבֵי רָעָתִֽי׃
5 Bari su zama kamar yayi a gaban iska, mala’ikan Ubangiji kuma yana korarsu;
יִֽהְיוּ כְּמֹץ לִפְנֵי־רוּחַ וּמַלְאַךְ יְהוָה דּוֹחֶֽה׃
6 bari hanyarsu tă yi duhu ta kuma yi santsi, mala’ikan Ubangiji kuma yana fafararsu.
יְֽהִי־דַרְכָּם חֹשֶׁךְ וַחֲלַקְלַקּוֹת וּמַלְאַךְ יְהוָה רֹדְפָֽם׃
7 Da yake sun ɓoye tarko domina ba dalili kuma babu dalili suka haƙa mini rami,
כִּֽי־חִנָּם טָֽמְנוּ־לִי שַׁחַת רִשְׁתָּם חִנָּם חָפְרוּ לְנַפְשִֽׁי׃
8 bari lalaci yă kama su ba zato, bari tarkon da suka ɓoye yă kama su, bari su fāɗa cikin ramin, yă kai ga lalacinsu.
תְּבוֹאֵהוּ שׁוֹאָה לֹֽא־יֵדָע וְרִשְׁתּוֹ אֲשֶׁר־טָמַן תִּלְכְּדוֹ בְּשׁוֹאָה יִפָּל־בָּֽהּ׃
9 Sa’an nan raina zai cika da farin ciki a cikin Ubangiji in yi kuma murna a cikin cetonsa.
וְנַפְשִׁי תָּגִיל בַּיהוָה תָּשִׂישׂ בִּישׁוּעָתֽוֹ׃
10 Dukan raina zai ce, “Wane ne kamar ka, ya Ubangiji? Ka kuɓutar da matalauta daga waɗanda suka fi ƙarfinsu, matalauta da masu bukata daga waɗanda suke musu fashi.”
כָּל עַצְמוֹתַי ׀ תֹּאמַרְנָה יְהוָה מִי כָמוֹךָ מַצִּיל עָנִי מֵחָזָק מִמֶּנּוּ וְעָנִי וְאֶבְיוֹן מִגֹּזְלֽוֹ׃
11 Shaidu marasa imani sun fito; suna mini tambaya a kan abubuwan da ban san kome a kai ba.
יְקוּמוּן עֵדֵי חָמָס אֲשֶׁר לֹא־יָדַעְתִּי יִשְׁאָלֽוּנִי׃
12 Suna sāka alherin da na yi musu da mugunta suka bar raina da nadama.
יְשַׁלְּמוּנִי רָעָה תַּחַת טוֹבָה שְׁכוֹל לְנַפְשִֽׁי׃
13 Duk da haka sa’ad da suke ciwo, na sanya rigar makoki na ƙasƙantar da kaina da azumi. Sa’ad da aka mayar mini da addu’o’i babu amsa,
וַאֲנִי ׀ בַּחֲלוֹתָם לְבוּשִׁי שָׂק עִנֵּיתִי בַצּוֹם נַפְשִׁי וּתְפִלָּתִי עַל־חֵיקִי תָשֽׁוּב׃
14 nakan yi ta yawo ina makoki sai ka ce yadda nake yi wa abokina ko ɗan’uwana. Nakan sunkuyar da kaina cikin baƙin ciki sai ka ce ina kuka domin mahaifiyata.
כְּרֵֽעַ־כְּאָח לִי הִתְהַלָּכְתִּי כַּאֲבֶל־אֵם קֹדֵר שַׁחֽוֹתִי׃
15 Amma sa’ad da na yi tuntuɓe, sukan taru suna murna; masu kai hari sun taru a kaina sa’ad da ban sani ba. Suna ɓata mini suna ba tsagaitawa.
וּבְצַלְעִי שָׂמְחוּ וְֽנֶאֱסָפוּ נֶאֶסְפוּ עָלַי נֵכִים וְלֹא יָדַעְתִּי קָֽרְעוּ וְלֹא־דָֽמּוּ׃
16 Kamar marasa sani Allah suna mini riyar ba’a; Suna hararata da ƙiyayya.
בְּחַנְפֵי לַעֲגֵי מָעוֹג חָרֹק עָלַי שִׁנֵּֽימוֹ׃
17 Ya Ubangiji, har yaushe za ka ci gaba da zuba ido kawai? Ka kuɓutar da raina daga farmakinsu, raina mai daraja daga waɗannan zakoki.
אֲדֹנָי כַּמָּה תִרְאֶה הָשִׁיבָה נַפְשִׁי מִשֹּׁאֵיהֶם מִכְּפִירִים יְחִידָתִֽי׃
18 Zan yi godiya cikin taro mai girma; cikin ɗumbun mutane zan yabe ka.
אוֹדְךָ בְּקָהָל רָב בְּעַם עָצוּם אֲהַֽלְלֶֽךָּ׃
19 Kada ka bar maƙaryatan nan, su yi farin ciki a kaina; kada ka bar waɗanda suke ƙina ba dalili, su ji daɗin baƙin cikina.
אַֽל־יִשְׂמְחוּ־לִי אֹיְבַי שֶׁקֶר שֹׂנְאַי חִנָּם יִקְרְצוּ־עָֽיִן׃
20 Ba sa maganar salama sukan ƙirƙiro zage-zagen ƙarya a kan waɗanda suka zama shiru a ƙasar.
כִּי לֹא שָׁלוֹם יְדַבֵּרוּ וְעַל רִגְעֵי־אֶרֶץ דִּבְרֵי מִרְמוֹת יַחֲשֹׁבֽוּן׃
21 Sukan wage mini bakinsu suna cewa, “Allah yă ƙara! Da idanunmu mun gani.”
וַיַּרְחִיבוּ עָלַי פִּיהֶם אָמְרוּ הֶאָח ׀ הֶאָח רָאֲתָה עֵינֵֽינוּ׃
22 Ya Ubangiji, ka ga wannan; kada ka yi shiru. Kada ka yi nisa da ni, ya Ubangiji.
רָאִיתָה יְהוָה אַֽל־תֶּחֱרַשׁ אֲדֹנָי אֲל־תִּרְחַק מִמֶּֽנִּי׃
23 Ka farka, ka kuma tashi ka kāre ni! Ka yi mini faɗa, ya Allahna da shugabana.
הָעִירָה וְהָקִיצָה לְמִשְׁפָּטִי אֱלֹהַי וַֽאדֹנָי לְרִיבִֽי׃
24 Ka nuna ni marar laifi ne ciki adalcinka, Ya Ubangiji Allahna; kada ka bari su yi farin ciki a kaina.
שָׁפְטֵנִי כְצִדְקְךָ יְהוָה אֱלֹהָי וְאַל־יִשְׂמְחוּ־לִֽי׃
25 Kada ka bari su ce wa kansu, “Allah yă ƙara, dā ma abin da mun so ke nan!” Ko su ce, “Mun haɗiye shi.”
אַל־יֹאמְרוּ בְלִבָּם הֶאָח נַפְשֵׁנוּ אַל־יֹאמְרוּ בִּֽלַּעֲנֽוּהוּ׃
26 Bari dukan waɗanda suke farin ciki a kaina a wahalata su sha kunya su kuma ruɗe; bari dukan waɗanda suke ɗaukar kansu sun fi ni su sha kunya da wulaƙanci.
יֵבֹשׁוּ וְיַחְפְּרוּ ׀ יַחְדָּו שְׂמֵחֵי רָעָתִי יִֽלְבְּשׁוּ־בֹשֶׁת וּכְלִמָּה הַֽמַּגְדִּילִים עָלָֽי׃
27 Bari waɗanda suke murna saboda nasarata su yi sowa don farin ciki da murna; bari kullum su riƙa cewa, “A ɗaukaka Ubangiji, wanda yake farin ciki da zaman lafiyar bawansa.”
יָרֹנּוּ וְיִשְׂמְחוּ חֲפֵצֵי צִדְקִי וְיֹאמְרוּ תָמִיד יִגְדַּל יְהוָה הֶחָפֵץ שְׁלוֹם עַבְדּֽוֹ׃
28 Harshena zai yi zancen adalcinka da kuma yabonka dukan yini.
וּלְשׁוֹנִי תֶּהְגֶּה צִדְקֶךָ כָּל־הַיּוֹם תְּהִלָּתֶֽךָ׃

< Zabura 35 >