< Zabura 34 >

1 Ta Dawuda. Sa’ad da ya yi kamar ya haukace a gaban Abimelek, Wanda ya kore shi, ya kuwa tafi. Zan gode wa Ubangiji kullayaumi; yabonsa kullum za su kasance a leɓunana.
Of David, when he feigned madness in the presence of Abimelech, who drove him away, and he left. I will bless the Lord at all times, in my mouth will his praise be forever.
2 Raina zai yi fariya a cikin Ubangiji; bari waɗanda suke wahala su ji su kuma yi farin ciki.
In the Lord will my heart make her boast, the humble will hear and be glad.
3 Ku ɗaukaka Ubangiji tare da ni; bari mu ɗaukaka sunansa tare.
O magnify the Lord with me and let us extol his name together.
4 Na nemi Ubangiji, ya kuwa amsa mini; ya cece ni daga dukan tsoro.
I sought the Lord, and, in answer, he saved me from all my terrors.
5 Waɗanda suke dubansa sukan haskaka; fuskokinsu ba sa rufuwa da kunya.
Look to him and you will be radiant, with faces unashamed.
6 Wannan matalauci ya yi kira, Ubangiji kuwa ya ji shi; ya cece shi daga dukan wahalarsa.
Here is one who was crushed, but cried and was heard by the Lord, and brought safe out of every trouble.
7 Mala’ikan Ubangiji ya kafa sansani kewaye da waɗanda suke tsoronsa, ya kuwa cece su.
The Lord’s angel encamps about those who fear him, and rescues them.
8 Ku gwada ku gani cewa Ubangiji yana da kyau; mai albarka ne mutumin da yake neman mafaka a gare shi.
O taste and see that the Lord is good, happy those who take refuge in him.
9 Ku ji tsoron Ubangiji, ku tsarkakansa, gama masu tsoronsa ba sa rasa kome.
Fear the Lord, all his people, for they who fear him lack nothing.
10 Zakoki za su iya rasa ƙarfi su kuma ji yunwa, amma waɗanda suke neman Ubangiji ba sa rasa abu mai kyau.
Even young lions may be poor and hungry, but those who seek the Lord will not lack any good thing.
11 Ku zo,’ya’yana, ku saurare ni; zan koya muku tsoron Ubangiji.
Come, children, listen to me. I will teach you the fear of the Lord.
12 Duk waninku da yake ƙaunar rayuwa yana kuma so yă ga kwanaki masu kyau,
Which of you is desirous of life, loves many and happy days?
13 ka kiyaye harshenka daga mugunta da kuma leɓunanku daga faɗar ƙarairayi.
Then guard your tongue from evil, and your lips from speaking deceit.
14 Juyo daga mugunta ku yi alheri; nemi salama ku kuma yi ƙoƙarin samunta.
Depart from evil, and do good; seek peace, and pursue it.
15 Idanun Ubangiji suna a kan masu adalci kuma kunnuwansa suna sauraran kukansu;
The eyes of the Lord are towards the righteous, his ears are towards their cry for help.
16 fuskar Ubangiji yana gāba da waɗanda suke aikata mugunta, don yă sa a manta da su a duniya.
The Lord sets his face against those who do evil, to root their memory out of the earth.
17 Adalai kan yi kuka, Ubangiji kuwa yakan ji su; yakan cece su daga dukan wahalarsu.
When righteous cry, they are heard by the Lord, and he saves them from all their distresses.
18 Ubangiji yana kusa da waɗanda suka karai ya kuma cece waɗanda aka ragargaza a ruhu.
The Lord is near to the broken-hearted, he helps those whose spirit is crushed.
19 Adali zai iya kasance da wahala da yawa, amma Ubangiji yakan cece shi daga dukansu;
Many misfortunes befall the righteous, but the Lord delivers them out of them all.
20 yakan tsare dukan ƙasusuwansa, ba ko ɗayansu da zai karye.
He guards all their bones, none are broken.
21 Mugunta zai kashe mugu; za a hukunta abokan gāban adalai.
Misfortune will slay the ungodly; those who hate the righteous are doomed.
22 Ubangiji yakan cece bayinsa; ba wanda yake neman mafaka a wurinsa da za a hukunta.
The Lord ransoms the life of his servants, and none will be doomed who takes refuge in him.

< Zabura 34 >