< Zabura 33 >
1 Ku rera da farin ciki ga Ubangiji ku adalai; daidai ne masu gaskiya su yabe shi.
Psalmus David. [Exsultate, justi, in Domino; rectos decet collaudatio.
2 Ku yabi Ubangiji da garaya; ku yi kiɗi gare shi da molo mai tsirkiya goma.
Confitemini Domino in cithara; in psalterio decem chordarum psallite illi.
3 Ku rera masa sabuwar waƙa; ku yi kiɗi da gwaninta, ku kuma yi sowa don farin ciki.
Cantate ei canticum novum; bene psallite ei in vociferatione.
4 Gama maganar Ubangiji daidai ne da kuma gaskiya; yana da aminci cikin kome da yake yi.
Quia rectum est verbum Domini, et omnia opera ejus in fide.
5 Ubangiji yana ƙaunar adalci duniya ta cika da ƙaunarsa marar ƙarewa.
Diligit misericordiam et judicium; misericordia Domini plena est terra.
6 Ta wurin maganar Ubangiji aka yi sammai, rundunar taurarinsu kuwa da numfashin bakinsa.
Verbo Domini cæli firmati sunt, et spiritu oris ejus omnis virtus eorum.
7 Ya tattara ruwan teku cikin tuluna; ya sa zurfafa cikin gidajen ajiya.
Congregans sicut in utre aquas maris; ponens in thesauris abyssos.
8 Bari dukan duniya ta ji tsoron Ubangiji; bari dukan mutanen duniya su girmama shi.
Timeat Dominum omnis terra; ab eo autem commoveantur omnes inhabitantes orbem.
9 Gama ya yi magana, abu ya kuwa kasance; ya umarta, ya kuwa tsaya daram.
Quoniam ipse dixit, et facta sunt; ipse mandavit et creata sunt.
10 Ubangiji yakan soke shirye-shiryen al’ummai; yakan wofintar da manufofin mutane.
Dominus dissipat consilia gentium; reprobat autem cogitationes populorum, et reprobat consilia principum.
11 Amma shirye-shiryen Ubangiji kan tsaya daram har abada, manufofin zuciyarsa kuwa har dukan zamanai.
Consilium autem Domini in æternum manet; cogitationes cordis ejus in generatione et generationem.
12 Mai farin ciki ce al’ummar da Allah ne Ubangijinta, mutanen da ya zaɓa don gādonsa.
Beata gens cujus est Dominus Deus ejus; populus quem elegit in hæreditatem sibi.
13 Daga sama Ubangiji ya duba ya kuwa ga dukan’yan adam;
De cælo respexit Dominus; vidit omnes filios hominum.
14 daga mazauninsa yana lura da dukan waɗanda suke zama a duniya,
De præparato habitaculo suo respexit super omnes qui habitant terram:
15 shi da ya yi zukatan duka, wanda yake kula da kome da suke yi.
qui finxit sigillatim corda eorum; qui intelligit omnia opera eorum.
16 Babu sarkin da ake ceto ta wurin yawan mayaƙansa; ba jarumin da kan kuɓuta ta wurin yawan ƙarfinsa.
Non salvatur rex per multam virtutem, et gigas non salvabitur in multitudine virtutis suæ.
17 Dogara a kan doki don ceto banza ne; duk da yawan ƙarfinsa ba ya ceto.
Fallax equus ad salutem; in abundantia autem virtutis suæ non salvabitur.
18 Amma idanun Ubangiji suna a kan wanda yake tsoronsa, a kan waɗanda suke sa zuciya cikin ƙaunarsa marar ƙarewa,
Ecce oculi Domini super metuentes eum, et in eis qui sperant super misericordia ejus:
19 don yă cece su daga mutuwa ya bar su da rai a lokacin yunwa.
ut eruat a morte animas eorum, et alat eos in fame.
20 Muna jiran Ubangiji da bege; shi ne taimakonmu da garkuwarmu.
Anima nostra sustinet Dominum, quoniam adjutor et protector noster est.
21 A cikinsa zukatanmu na farin ciki, gama mun dogara cikin sunansa mai tsarki.
Quia in eo lætabitur cor nostrum, et in nomine sancto ejus speravimus.
22 Bari ƙaunarka marar ƙarewa ta zauna a kanmu, ya Ubangiji, ko ma da muke sa begenmu a gare ka.
Fiat misericordia tua, Domine, super nos, quemadmodum speravimus in te.]