< Zabura 31 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. A gare ka, ya Ubangiji, na nemi mafaka; kada ka bari in taɓa shan kunya; ka cece ni cikin rahamarka.
למנצח מזמור לדוד בך יהוה חסיתי אל אבושה לעולם בצדקתך פלטני׃
2 Ka juye kunnenka gare ni, ka zo da sauri ka cece ni; ka zama dutsen mafakata, mafaka mai ƙarfi na cetona.
הטה אלי אזנך מהרה הצילני היה לי לצור מעוז לבית מצודות להושיעני׃
3 Da yake kai ne dutsena da kuma kagarata, saboda sunanka ka bi da ni ka kuma jagorance ni.
כי סלעי ומצודתי אתה ולמען שמך תנחני ותנהלני׃
4 Ka’yantar da ni daga tarkon da aka sa mini, gama kai ne mafakata.
תוציאני מרשת זו טמנו לי כי אתה מעוזי׃
5 Cikin hannuwanka na miƙa ruhuna; ka cece ni, ya Ubangiji Allah na gaskiya.
בידך אפקיד רוחי פדיתה אותי יהוה אל אמת׃
6 Na ƙi waɗanda suke manne wa gumakan banza; na dogara ga Ubangiji.
שנאתי השמרים הבלי שוא ואני אל יהוה בטחתי׃
7 Zan yi murna in kuma yi farin ciki a cikin ƙaunarka, gama ka ga azabata ka kuma san wahalar raina.
אגילה ואשמחה בחסדך אשר ראית את עניי ידעת בצרות נפשי׃
8 Ba ka ba da ni ga abokin gāba ba amma ka sa ƙafafuna a wuri mai sarari.
ולא הסגרתני ביד אויב העמדת במרחב רגלי׃
9 Ka yi mini jinƙai, ya Ubangiji, gama ina cikin damuwa; idanuna sun gaji da baƙin ciki, raina da jikina sun tafke tilis.
חנני יהוה כי צר לי עששה בכעס עיני נפשי ובטני׃
10 Baƙin ciki ya rufe raina shekaruna sun cika da nishi; ƙarfina ya karai saboda azaba, ƙasusuwana kuma sun gaji tiƙis.
כי כלו ביגון חיי ושנותי באנחה כשל בעוני כחי ועצמי עששו׃
11 Saboda dukan abokan gābana, Na zama tamƙar abin reni na maƙwabtana; na zama abin tsoro ga abokaina, waɗanda suka gan ni a titi sukan gudu daga gare ni.
מכל צררי הייתי חרפה ולשכני מאד ופחד למידעי ראי בחוץ נדדו ממני׃
12 An manta da ni sai ka ce na mutu; na zama kamar fasasshen kasko.
נשכחתי כמת מלב הייתי ככלי אבד׃
13 Gama nakan ji raɗe-raɗen mutane masu yawa; akwai tsoro a kowane gefe; suna ƙulla maƙarƙashiya a kaina suna shirya su ɗauke raina.
כי שמעתי דבת רבים מגור מסביב בהוסדם יחד עלי לקחת נפשי זממו׃
14 Amma na dogara gare ka, ya Ubangiji; na ce, “Kai ne Allahna.”
ואני עליך בטחתי יהוה אמרתי אלהי אתה׃
15 Lokutana suna a hannuwanka; ka cece ni daga abokan gābana da kuma daga waɗanda suke fafara ta.
בידך עתתי הצילני מיד אויבי ומרדפי׃
16 Bari fuskarka ta haskaka a kan bawanka; ka cece ni da ƙaunarka marar ƙarewa.
האירה פניך על עבדך הושיעני בחסדך׃
17 Kada ka bari in sha kunya, ya Ubangiji, gama na yi kuka gare ka; amma bari mugaye su sha kunya su kuma kwanta shiru a cikin kabari. (Sheol h7585)
יהוה אל אבושה כי קראתיך יבשו רשעים ידמו לשאול׃ (Sheol h7585)
18 Bari a rufe leɓunan ƙarairayinsu, gama da fariya da reni suna magana da girman kai a kan adalai.
תאלמנה שפתי שקר הדברות על צדיק עתק בגאוה ובוז׃
19 Alherinka da girma yake, wanda ka ajiye domin waɗanda suke tsoronka, wanda ka mayar a gaban mutane a kan waɗanda suke neman mafaka daga gare ka.
מה רב טובך אשר צפנת ליראיך פעלת לחסים בך נגד בני אדם׃
20 Cikin inuwar kasancewarka ka ɓoye su daga makircin mutane; a wurin zamanka ka kiyaye su lafiya daga harsuna masu zagi.
תסתירם בסתר פניך מרכסי איש תצפנם בסכה מריב לשנות׃
21 Yabo ya tabbata ga Ubangiji, gama ya nuna ƙaunarsa mai banmamaki gare ni sa’ad da aka yi mini kwanto kewaye da birni.
ברוך יהוה כי הפליא חסדו לי בעיר מצור׃
22 Cikin tsorona na ce, “An yanke ni daga gabanka!” Duk da haka ka ji kukata na neman jinƙai sa’ad da na kira gare ka don taimako.
ואני אמרתי בחפזי נגרזתי מנגד עיניך אכן שמעת קול תחנוני בשועי אליך׃
23 Ku ƙaunaci Ubangiji, dukanku tsarkakansa! Ubangiji yakan adana amintattu, amma masu girman kai yakan sāka musu cikakke.
אהבו את יהוה כל חסידיו אמונים נצר יהוה ומשלם על יתר עשה גאוה׃
24 Ku yi ƙarfin hali ku kuma ƙarfafa, dukanku masu sa bege a kan Ubangiji.
חזקו ויאמץ לבבכם כל המיחלים ליהוה׃

< Zabura 31 >