< Zabura 30 >
1 Zabura ce. Wata waƙa. Don keɓewar haikali. Ta Dawuda. Zan girmama ka Ya Ubangiji, gama ka tsamo ni daga zurfafa ba ka bar abokan gābana sun yi farin ciki a kaina ba.
A psalm of David. A song for the dedication of the Temple. I will extol you, O Lord, because you have lifted me up, and not suffered my foes to rejoice over me.
2 Ya Ubangiji Allahna, na yi kira gare ka don taimako ka kuwa warkar da ni.
I cried to you for help, O Lord my God, and you healed me.
3 Ya Ubangiji, ka dawo da ni daga kabari; ka kiyaye ni daga gangarawa zuwa cikin rami. (Sheol )
You have brought me up, Lord, from Sheol, from my way to the pit back to life you have called me. (Sheol )
4 Ku rera ga Ubangiji, ku tsarkakansa; ku yabi sunansa mai tsarki.
Sing praise to the Lord, faithful people; give thanks to his holy name.
5 Gama fushinsa na ɗan lokaci ne amma alherinsa har matuƙa ne; mai yiwuwa a yi kuka da dare amma farin ciki kan zo da safe.
For his anger lasts only a moment, his favour endures for a lifetime. Weeping may lodge for the night, but the morning brings shouts of joy.
6 Sa’ad da nake lafiya, na ce, “Ba zan jijjigu ba.”
When all went well, I imagined that never should I be shaken.
7 Ya Ubangiji, sa’ad da ka yi mini alheri, ka sa katangar dutsena ya tsaya daram; amma sa’ad da ka ɓoye fuskarka, sai in cika da tsoro.
For by your favour, O Lord, you had set me on mountains strong: but you hide your face, and I was confounded.
8 A gare ka, ya Ubangiji, na yi kira; a gare ka Ubangiji na yi kukan neman jinƙai.
Then to you, Lord, I cried, to the Lord I begged for mercy,
9 “Wace riba ce a hallakata, a kuma gangarawa ta zuwa cikin rami? Ƙura za tă yabe ka ne? Za tă iya yin shelar amincinka?
‘What profit is there in my blood, if I go down to the pit? Can you be praised by dust? Can it tell of your faithfulness?
10 Ka ji, ya Ubangiji, ka kuwa yi mini jinƙai; Ya Ubangiji, ka zama taimakona.”
Hear, Lord, and show me your favour, Lord be a helper to me.’
11 Ka mai da kukata ta zama rawa; ka tuɓe rigar makokina ka sa mini na farin ciki,
You have turned my mourning to dancing; my sackcloth you have unloosed, and clothed me with joy:
12 don zuciyata za tă iya rera gare ka ba kuwa za tă yi shiru ba. Ya Ubangiji Allahna, zan yi maka godiya har abada.
that unceasingly I should sing your praise, and give thanks to you, Lord my God, forever.