< Zabura 3 >
1 Zabura ta Dawuda. Sa’ad da ya gudu daga ɗansa Absalom. Ya Ubangiji, abokan gābana nawa ne! Su nawa suke gāba da ni!
2 Da yawa suna magana a kaina suna cewa, “Allah ba zai cece shi ba.” (Sela)
3 Amma kai ne garkuwa kewaye da ni, ya Ubangiji; ka ba ni ɗaukaka ka kuma ɗaga kaina.
4 Ga Ubangiji na yi kuka mai ƙarfi, ya kuwa amsa mini daga tudunsa mai tsarki. (Sela)
5 Na kwanta na yi barci; na kuma farka, gama Ubangiji yana kiyaye ni.
6 Ba zan ji tsoro ko dubu goma suka ja dāgā gāba da ni a kowane gefe ba.
7 Ka tashi Ya Ubangiji! Ka cece ni, ya Allahna! Ka bugi dukan abokan gābana a muƙamuƙi; ka kakkarya haƙoran mugaye.
8 Daga wurin Ubangiji ne ceto kan zo. Bari albarkanka yă kasance a kan mutanenka. (Sela)