< Zabura 25 >

1 Ta Dawuda. A gare ka Ya Ubangiji, na miƙa raina.
לדוד אליך יהוה נפשי אשא
2 A gare ka na dogara, ya Allahna. Kada ka bari in sha kunya, ko ka bar abokan gābana su yi nasara a kaina.
אלהי--בך בטחתי אל-אבושה אל-יעלצו אויבי לי
3 Ba wanda yake sa bege a gare ka da zai taɓa shan kunya, amma za su sha kunya su da suke tayarwa babu dalili.
גם כל-קויך לא יבשו יבשו הבוגדים ריקם
4 Ka nuna mini hanyoyinka, ya Ubangiji, ka koya mini hanyoyinka;
דרכיך יהוה הודיעני ארחותיך למדני
5 ka bi da ni cikin gaskiyarka ka kuma koya mini, gama kai ne Allah Mai cetona, kuma begena yana a kanka dukan yini.
הדריכני באמתך ולמדני-- כי-אתה אלהי ישעי אותך קויתי כל-היום
6 Ka tuna, ya Ubangiji da jinƙai da kuma ƙaunarka mai girma, gama suna nan tun dā.
זכר-רחמיך יהוה וחסדיך כי מעולם המה
7 Kada ka tuna da zunuban ƙuruciyata da kuma hanyoyin tawayena; bisa ga ƙaunarka ka tuna da ni, gama kai nagari ne, ya Ubangiji.
חטאות נעורי ופשעי-- אל-תזכר כחסדך זכר-לי-אתה-- למען טובך יהוה
8 Ubangiji nagari da mai adalci ne; saboda haka yakan koyar da masu zunubi a hanyoyinsa.
טוב-וישר יהוה על-כן יורה חטאים בדרך
9 Yakan bi da masu tawali’u cikin abin da yake daidai ya kuma koyar da su hanyoyinsa.
ידרך ענוים במשפט וילמד ענוים דרכו
10 Dukan hanyoyin Ubangiji ƙaunatattu ne da kuma aminci ga waɗanda suke kiyaye abin da alkawari ya bukaci.
כל-ארחות יהוה חסד ואמת-- לנצרי בריתו ועדתיו
11 Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka gafarta laifina, ko da yake mai girma ne.
למען-שמך יהוה וסלחת לעוני כי רב-הוא
12 To wane ne mai tsoron Ubangiji? Zai koyar da shi a hanyar da ya zaɓa masa.
מי-זה האיש ירא יהוה-- יורנו בדרך יבחר
13 Zai ci kwanakinsa a wadace, kuma zuriyarsa za su gāji ƙasar.
נפשו בטוב תלין וזרעו יירש ארץ
14 Ubangiji yakan amince da waɗanda suke tsoronsa; yakan sa su san alkawarinsa.
סוד יהוה ליראיו ובריתו להודיעם
15 Idanuna kullum suna a kan Ubangiji, gama shi ne kaɗai zai kuɓutar da ƙafafuna daga tarko.
עיני תמיד אל-יהוה כי הוא-יוציא מרשת רגלי
16 Ka juye wurina ka kuma yi mini jinƙai, gama na kaɗaice ina kuma wahala.
פנה-אלי וחנני כי-יחיד ועני אני
17 Damuwoyin zuciyata sun ninka; ka’yantar da ni daga wahalata.
צרות לבבי הרחיבו ממצוקותי הוציאני
18 Ka dubi wahalata da kuma azabata ka ɗauke mini dukan zunubaina.
ראה עניי ועמלי ושא לכל-חטאותי
19 Dubi yadda abokan gābana sun ƙaru da kuma yadda suka ƙara ƙina!
ראה-איבי כי-רבו ושנאת חמס שנאוני
20 Ka tsare raina ka kuma kuɓutar da ni; kada ka bari in sha kunya, gama na nemi mafaka daga gare ka.
שמרה נפשי והצילני אל-אבוש כי-חסיתי בך
21 Bari mutunci da adalci su tsare ni, domin begena yana a kanka.
תם-וישר יצרוני כי קויתיך
22 Ka fanshi Isra’ila, ya Allah, daga dukan wahalarsu!
פדה אלהים את-ישראל-- מכל צרותיו

< Zabura 25 >