< Zabura 22 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da salon “Matar Zomon Safiya.” Zabura ta Dawuda. Ya Allahna, ya Allahna, don me ka yashe ni? Me ya sa ka yi nisa da cetona, ka yi nesa daga kalmomin nishina?
2 Ya Allahna, na yi kuka da rana, amma ba ka amsa ba, da dare kuma ban yi shiru ba.
3 Duk da haka kana a kursiyi a matsayin Mai Tsarkin nan; kai ne yabon Isra’ila.
4 A gare ka ne kakanninmu suka sa bege; sun dogara ka kuwa cece su.
5 Sun yi kuka gare ka suka kuma sami ceto; a gare ka suka dogara kuma ba su sha kunya ba.
6 Amma ni dai tsutsa ne ba mutum ba, wanda mutane suke yi wa ba’a suka kuma rena shi.
7 Duk wanda ya gan ni yakan yi mini ba’a; suna yin mini ashar, suna kaɗa kansu suna cewa,
8 “Ya dogara ga Ubangiji; bari Ubangiji yă cece shi. Bari yă cece shi, da yake yana jin daɗinsa.”
9 Duk da haka ka fitar da ni daga ciki; ka sa na dogara gare ka, ko ma a ƙirjin mahaifiyata.
10 Daga haihuwa an jefa ni a kanka; daga cikin mahaifiyata kai ne Allahna.
11 Kada ka yi nesa da ni, gama wahala na kusa kuma babu wani da zai taimaka.
12 Bijimai masu yawa sun kewaye ni; bijimai masu ƙarfi na Bashan sun sa ni a tsaka.
13 Zakoki masu ruri suna yayyage abin da suka kama sun buɗe bakunansu a kaina.
14 An zubar da ni kamar ruwa, kuma dukan ƙasusuwana sun fiffito daga mahaɗai. Zuciyata ta zama kaki; ta narke a cikina.
15 Ƙarfina ya bushe kamar kasko, harshena kuma ya manne wa dasashina na sama; ka kwantar da ni a ƙurar mutuwa.
16 Karnuka sun kewaye ni; ƙungiyar mugaye sun sa ni a tsaka, sun soki hannuwana da ƙafafuna.
17 Zan iya ƙirga ƙasusuwana; mutane suna farin ciki a kaina.
18 Sun raba rigunana a tsakaninsu suka kuma jefa ƙuri’a a kan rigunana.
19 Amma kai, ya Ubangiji, kada ka yi nisa; Ya Ƙarfina zo da sauri don ka taimake ni.
20 Ka ceci raina daga takobi, raina mai daraja daga ikon karnuka.
21 Ka cece ni daga bakin zakoki; ka cece ni daga ƙahonin ɓauna.
22 Zan furta sunanka ga’yan’uwana; cikin taron masu sujada zan yabe ka.
23 Ku da kuke tsoron Ubangiji, ku yabe shi! Dukanku zuriyar Yaƙub, ku girmama shi! Ku girmama shi, dukanku zuriyar Isra’ila!
24 Gama bai rena ko yă ƙyale wahalar masu shan wuya ba; bai ɓoye fuskarsa daga gare shi ba amma ya saurari kukansa na neman taimako.
25 Daga gare ka yabona yake zuwa cikin babban taro; a gaban waɗanda suke tsoronka zan cika alkawarina.
26 Matalauta za su ci su ƙoshi; su da suke neman Ubangiji za su yabe shi, bari zukatanku su rayu har abada!
27 Dukan iyakokin duniya za su tuna su kuma juya ga Ubangiji, kuma dukan iyalan al’ummai za su rusuna a gabansa,
28 gama mulki na Ubangiji ne kuma yana mulki a bisa al’ummai.
29 Dukan attajiran duniya za su yi biki su kuma yi sujada; dukan waɗanda suka gangara zuwa ƙura za su durƙusa a gabansa, waɗanda ba za su iya bar kansu da rai ba.
30 Zuriya masu zuwa za su yi masa hidima; za a faɗa wa zuriya na nan gaba game da Ubangiji.
31 Za su yi shelar adalcinsa ga mutanen da ba a riga an haifa ba, gama ya aikata shi.