< Zabura 21 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, sarki yana farin ciki cikin ƙarfinka. Yana farin cikinsa ƙwarai cikin nasarorin da ka ba shi!
Unto the end. A psalm for David. In thy strength, O Lord, the king shall joy; and in thy salvation he shall rejoice exceedingly.
2 Ka biya masa bukatar zuciyarsa ba ka kuwa hana masa roƙon da ya yi da leɓunansa ba. (Sela)
Thou hast given him his heart’s desire: and hast not withholden from him the will of his lips.
3 Ka marabce shi da yalwar albarka ka kuma sa masa rawanin zallan zinariya a kansa.
For thou hast prevented him with blessings of sweetness: thou hast set on his head a crown of precious stones.
4 Ya nemi ka ba shi rai, ka kuwa ba shi, tsawo kwanaki, har abada abadin
He asked life of thee: and thou hast given him length of days for ever and ever.
5 Ta wurin nasarorin da ka ba shi, ɗaukakarsa mai girma ce; ka mayar masa ɗaukaka da kuma suna.
His glory is great in thy salvation: glory and great beauty shalt thou lay upon him.
6 Tabbatacce ka ba shi madawwamiyar albarka ka kuma sa shi murna da farin cikin kasancewarka.
For thou shalt give him to be a blessing for ever and ever: thou shalt make him joyful in gladness with thy countenance.
7 Gama sarki ya dogara gare ka Ubangiji ta wurin ƙauna marar ƙarewa ta Mafi Ɗaukaka ba zai jijjigu ba.
For the king hopeth in the Lord: and through the mercy of the most High he shall not be moved.
8 Hannunka zai kakkama dukan abokan gābanka; hannunka na dama zai kakkama masu ƙinka.
Let thy hand be found by all thy enemies: let thy right hand find out all them that hate thee.
9 A lokacin bayyanarka za ka sa su zama kamar wutar matoya. Cikin fushinsa Ubangiji zai haɗiye su, kuma wutarsa za tă cinye su.
Thou shalt make them as an oven of fire, in the time of thy anger: the Lord shall trouble them in his wrath, and fire shall devour them.
10 Za ka hallaka’ya’yansu daga duniya, zuriyarsu kuma daga’yan adam.
Their fruit shalt thou destroy from the earth: and their seed from among the children of men.
11 Ko da yake suna shirya maka mugunta suna kuma ƙirƙiro mugayen dabaru, ba za su yi nasara ba;
For they have intended evils against thee: they have devised counsels which they have not been able to establish.
12 gama za ka sa su juye bayansu sa’ad da ka auna su da bakan da ka ja.
For thou shalt make them turn their back: in thy remnants thou shalt prepare their face.
13 Ka sami ɗaukaka, ya Ubangiji cikin ƙarfinka; za mu rera mu kuma yabi ikonka.
Be thou exalted, O Lord, in thy own strength: we will sing and praise thy power.