< Zabura 2 >

1 Me ya sa ƙasashe suke haɗa baki mutane kuma suke ƙulla shawarwarin banza?
למה רגשו גוים ולאמים יהגו-ריק
2 Sarakunan duniya sun ɗauki matsayi masu mulki sun taru gaba ɗaya suna gāba da Ubangiji da kuma Shafaffensa.
יתיצבו מלכי-ארץ-- ורוזנים נוסדו-יחד על-יהוה ועל-משיחו
3 Suna cewa, “Bari mu tsittsinke sarƙoƙinsu, mu kuma’yantar da kamammu daga kangin bautar Allah.”
ננתקה את-מוסרותימו ונשליכה ממנו עבתימו
4 Mai zama a kursiyi a sama yana dariya; Ubangiji yana musu ba’a.
יושב בשמים ישחק אדני ילעג-למו
5 Sa’an nan ya tsawata musu cikin fushinsa ya kuma razanar da su cikin hasalarsa, yana cewa,
אז ידבר אלימו באפו ובחרונו יבהלמו
6 “Na kafa Sarkina a kan kursiyi a kan Sihiyona, dutsena mai tsarki.”
ואני נסכתי מלכי על-ציון הר-קדשי
7 Sarki ya yi shelar umarnin Ubangiji. Ubangiji ya ce mini, “Kai Ɗana ne; yau na zama Mahaifinka.
אספרה אל-חק יהוה אמר אלי בני אתה--אני היום ילדתיך
8 Ka tambaye ni zan kuwa sa al’ummai su zama gādonka, iyakokin duniya su zama mallakarka.
שאל ממני--ואתנה גוים נחלתך ואחזתך אפסי-ארץ
9 Za ka yi mulkinsu da sandan ƙarfe; za ka farfashe su kucu-kucu kamar tukunyar laka.”
תרעם בשבט ברזל ככלי יוצר תנפצם
10 Saboda haka, ku sarakuna, ku yi wayo; ku shiga hankalinku, ku masu mulkin duniya.
ועתה מלכים השכילו הוסרו שפטי ארץ
11 Ku bauta wa Ubangiji da tsoro ku kuma yi farin ciki kuna rawar jiki.
עבדו את-יהוה ביראה וגילו ברעדה
12 Ku sumbaci Ɗan, don kada yă yi fushi ku hallaka a abubuwan da kuke yi, gama fushinsa zai iya kuna farat ɗaya. Masu farin ciki ne dukan waɗanda suke neman mafaka daga gare shi.
נשקו-בר פן-יאנף ותאבדו דרך-- כי-יבער כמעט אפו אשרי כל-חוסי בו

< Zabura 2 >