< Zabura 19 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sammai suna shelar ɗaukakar Allah; sararin sama suna furta aikin hannuwansa.
2 Kowace rana tana yin jawabi; kowane dare yana nuna sani.
3 Ba magana, ba kalmar da aka hurta, ba wani amon da aka ji daga gare su.
4 Duk da haka muryarsu tana kaiwa ga dukan duniya, kalmominsu zuwa iyakokin duniya. A sammai Allah ya kafa tenti domin rana,
5 wanda yake kamar ango mai fitowa daga rumfarsa, kamar gwani ɗan wasan da yake farin ciki yă yi tsere.
6 Takan taso daga ƙarshen sammai ta kewaye zuwa wancan; babu abin da yake ɓuya wa zafinta.
7 Dokar Ubangiji cikakkiya ce, takan wartsakar da rai. Farillan Ubangiji abin dogara ne, suna mai da hikima da sauƙi.
8 Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne, suna ba da farin ciki ga zuciya. Umarnan Ubangiji haske ne suna ba da haske ga idanu.
9 Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya, zai kasance har abada. Farillan Ubangiji tabbatattu ne, kuma gaba ɗaya masu adalci ne.
10 Sun fi zinariya daraja, fiye da zalla zinariya nesa; sun fi zuma zaƙi fiye da zuma daga kaki.
11 Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka; a kiyaye su akwai lada mai girma.
12 Wane ne zai iya rabe kurakuransa? Ya gafarta ɓoyayyun laifofinsa.
13 Ka kiyaye bawanka daga zunubin ganganci; kada ka bari su yi mulki a kaina. Ta haka zan zama marar laifi; marar laifi na babban tawaye.
14 Bari kalmomin bakina da tunanin zuciyata su zama abin gamsuwa a gabanka, Ya Ubangiji, Dutsena da Mai fansata.