< Zabura 18 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda bawan Ubangiji. Ya rera ta ga Ubangiji kalmomin wannan waƙa sa’ad da Ubangiji ya cece shi daga hannun dukan abokan gābansa da kuma daga hannun Shawulu, ya ce, Ina ƙaunarka, ya Ubangiji, ƙarfina.
2 Ubangiji shi ne dutsena, kagarata da kuma mai cetona; Allahna shi ne dutsena, a gare shi nake neman mafaka. Shi ne garkuwata da ƙahon cetona, mafakata.
3 Na kira ga Ubangiji, wanda ya cancanci yabo, na kuwa kuɓuta daga abokan gābana.
4 Igiyoyin mutuwa sun shaƙe ni; rigyawan hallaka sun sha kaina.
5 Igiyoyin mutuwa sun nannaɗe kewaye da ni; tarkon mutuwa ya yi mini arangama. (Sheol )
6 Cikin wahalata na yi kira ga Ubangiji; Na yi kuka ga Allahna don taimako. A Haikalinsa ya ji muryata, Kukana na neman taimako ya kai kunnensa.
7 Ƙasa ta yi rawa ta kuma girgiza, tussan duwatsu sun girgiza; sun yi rawa domin ya yi fushi.
8 Hayaƙi ya tashi daga kafan hancinsa; wuta mai ci daga bakinsa, garwashi wuta mai ci daga bakinsa.
9 Ya buɗe sammai ya sauko; baƙaƙen gizagizai suna a ƙarƙashin ƙafafunsa.
10 Ya hau kerubobi ya kuma yi firiya; ya yi shawagi a fikafikan iska.
11 Ya mai da duhu abin rufuwarsa, rumfa kewaye da shi, baƙaƙen gizagizan ruwan sama na sarari,
12 daga cikin hasken kasancewarsa gizagizai suka yi gaba, da ƙanƙara da kuma walƙiya.
13 Ubangiji ya yi tsawa daga sama; muryar Mafi Ɗaukaka ya yi kāra.
14 Ya harba kibiyoyinsa ya kuma watsar da abokan gāba, walƙiya mai girma ya fafare su.
15 Kwarin teku sun bayyana tussan duniya sun bayyana a fili sa’ad da ka tsawata, ya Ubangiji, sa’ad da ka numfasa daga hancinka.
16 Ya miƙa hannunsa daga sama ya kama ni; ya ja ni daga zurfin ruwaye.
17 Ya cece ni daga abokin gābana mai ƙarfi, daga abokan gābana, waɗanda suka fi ƙarfina.
18 Sun yi arangama da ni a ranar masifa, amma Ubangiji ya zama mai taimakona.
19 Ya fitar da ni zuwa wuri mai sarari; ya kuɓutar da ni, gama yana jin daɗina.
20 Ubangiji ya yi haka da ni bisa ga adalcina; bisa ga tsabtar hannuwana ya ba ni lada.
21 Gama na kiyaye hanyoyin Ubangiji; ban yi mugunta ta wurin juyewa daga Allahna ba.
22 Dukan dokokinsa suna a gābana; ban juye daga ƙa’idodinsa ba.
23 Na kasance marar laifi a gabansa na kuma kiyaye kaina daga zunubi.
24 Ubangiji ya ba ni lada bisa ga adalcina, bisa ga tsabtan hannuwana a gabansa.
25 Ga mai aminci ka nuna kanka mai aminci, ga marar laifi ka nuna kanka marar laifi,
26 ga mai tsabta ka nuna kanka mai tsabta, amma ga karkatacce, ka nuna kanka mai wayo.
27 Kakan cece mai sauƙinkai amma kakan ƙasƙantar da masu girman kai.
28 Kai Ya Ubangiji, ka sa fitilata ta yi ta ci; Allahna ya mai da duhu ya zama haske.
29 Da taimakonka zan iya fāɗa wa runduna; tare da Allahna zan iya rinjayi katanga.
30 Game da Allah kuwa, hanyarsa cikakkiya ce; maganar Ubangiji marar kuskure ne. Shi garkuwa ne ga dukan waɗanda suke neman mafaka a gare shi.
31 Gama wane ne Allah in ba Ubangiji ba? Wane ne kuwa Dutse in ba Allahnmu ba?
32 Allah ne ya ƙarfafa ni da ƙarfi ya kuma sa hanyarta ta zama cikakkiya.
33 Ya sa ƙafafuna kamar ƙafafun barewa; ya sa na iya tsaya a kan ƙwanƙoli.
34 Ya horar da hannuwana don yaƙi; hannuwana za su iya tanƙware bakan tagulla.
35 Ka ba ni garkuwar nasara, kuma hannunka na dama yana riƙe ni; ya sunkuya don ka mai da ni mai girma.
36 Ka fadada hanyar da yake a ƙarƙashina, don kada ɗiɗɗigena yă juya.
37 Na bi abokan gābana na kuma cim musu; ban juya ba sai da na hallaka su.
38 Na ragargaza su har ba za su iya tashi ba; sun fāɗi a ƙarƙashin ƙafafuna.
39 Ka ƙarfafa ni da ƙarfi saboda yaƙi; ka sa abokan gābana suka rusuna mini.
40 Ka sa abokan gābana suka juya suka gudu, na kuma hallaka abokan gābana.
41 Sun nemi taimako, amma ba su sami wanda zai cece su ba, ga Ubangiji, amma bai amsa ba.
42 Na murƙushe su kamar ƙura mai laushi da iska ke kwashewa; na zubar da su kamar laka a tituna.
43 Ka cece ni daga harin mutane; ka mai da ni kan al’ummai. Mutanen da ban sani ba sun zama bayina,
44 da zarar sun ji ni, sukan yi mini biyayya; baƙi suna rusuna a gabana.
45 Duk sukan karai; suna zuwa da rawan jiki daga mafakansu.
46 Ubangiji mai rai ne! Yabo ya tabbata ga Dutsena! Girma ya tabbata ga Allah Mai cetona!
47 Shi ne Allah mai sāka mini, wanda yake sa al’ummai a ƙarƙashina,
48 wanda yakan cece ni daga abokan gābana. Ana girmama ka bisa abokan gābana; daga masu tā-da-na-zaune-tsaye ka kuɓutar da ni.
49 Saboda haka zan yabe ka a cikin al’ummai, ya Ubangiji; zan rera yabai ga sunanka.
50 Yakan ba sarkinsa nasarori; yakan nuna alheri marar ƙarewa ga shafaffensa, ga Dawuda da zuriyarsa har abada.