< Zabura 15 >
1 Zabura ta Dawuda. Ubangiji, wa zai zauna cikin wuri mai tsarkinka? Wa zai zauna a kan tudunka mai tsarki?
Господе! Ко може седети у сеници Твојој? Ко може наставати на светој гори Твојој?
2 Sai wanda ba shi da laifi kuma yana yin abin da yake daidai, wanda yake faɗin gaskiya daga zuciyarsa
Ко ходи без мане, твори правду, и говори истину из срца свог;
3 ba ya kuwa ɓata sunan wani da harshensa, wanda ba ya yi wa maƙwabcinsa mugunta ba ya kuwa baza jita-jita a kan ɗan’uwansa,
Ко не опада језиком својим, не чини другом зло, и не ружи ближњег свог;
4 wanda yake ƙin mugun mutum amma yakan girmama masu tsoron Ubangiji, yakan cika alkawarinsa ko da ma ya zafe shi,
Ко не гледа оног кога је Бог одбацио, него поштује оне који се боје Господа; ко се куне ближњему па не пориче;
5 wanda yake ba da rance ba tare da ruwa ba kuma ba ya karɓan cin hanci don yă kā da marar laifi. Shi wanda yake yin waɗannan abubuwa ba zai taɓa jijjiguwa ba.
Ко не даје сребро своје на добит, и не прима мито на правога. Ко овако ради, неће посрнути довека.