< Zabura 148 >

1 Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji daga sammai, yabe shi a bisa sammai.
Praise ye the LORD. Praise ye the LORD from the heavens: praise him in the heights.
2 Yabe shi, dukanku mala’ikunsa, yabe shi, dukanku rundunarsa na sama.
Praise ye him, all his angels: praise ye him, all his hosts.
3 Yabe shi, rana da wata, yabe shi, dukanku taurari masu haskakawa.
Praise ye him, sun and moon: praise him, all ye stars of light.
4 Yabe shi, ku bisa sammai da kuma ku ruwan bisa sarari.
Praise him, ye heavens of heavens, and ye waters that [be] above the heavens.
5 Bari su yabi sunan Ubangiji, gama ya umarta aka kuwa halicce su.
Let them praise the name of the LORD: for he commanded, and they were created.
6 Ya sa su a wurarensu har abada abadin; ya ba da umarnin da ba zai taɓa shuɗe ba.
He hath also stablished them for ever and ever: he hath made a decree which shall not pass.
7 Yabi Ubangiji daga duniya, ku manyan halittun teku da kuma dukan zurfafan teku,
Praise the LORD from the earth, ye dragons, and all deeps:
8 walƙiya da ƙanƙara, dusar ƙanƙara da gizagizai, hadirin iskar da suke biyayya da umarnansa,
Fire, and hail; snow, and vapour; stormy wind fulfilling his word:
9 ku duwatsu da dukan tuddai, itatuwa masu’ya’ya da dukan al’ul,
Mountains, and all hills; fruitful trees, and all cedars:
10 namun jeji da dukan dabbobin gida, ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,
Beasts, and all cattle; creeping things, and flying fowl:
11 sarakunan duniya da dukan al’ummai, ku sarakuna da dukan masu mulkin duniya,
Kings of the earth, and all people; princes, and all judges of the earth:
12 samari da’yan mata, tsofaffi da yara.
Both young men, and maidens; old men, and children:
13 Bari su yabi sunan Ubangiji, gama sunansa ne kaɗai mafi ɗaukaka; darajarsa ta fi ƙarfin duniya da sammai.
Let them praise the name of the LORD: for his name alone is excellent; his glory [is] above the earth and heaven.
14 Ya tayar wa mutanensa ƙaho, yabon dukan tsarkakansa, na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa. Yabi Ubangiji.
He also exalteth the horn of his people, the praise of all his saints; [even] of the children of Israel, a people near unto him. Praise ye the LORD.

< Zabura 148 >