< Zabura 147 >

1 Yabi Ubangiji. Yana da kyau a rera yabai ga Allahnmu, abu mai daɗi ne daidai ne kuma a yabe shi!
הַלְלוּ ־ יָהּ ׀ כִּי־טוֹב זַמְּרָה אֱלֹהֵינוּ כִּי־נָעִים נָאוָה תְהִלָּֽה׃
2 Ubangiji ya gina Urushalima; ya tattara kamammu na Isra’ilan da aka kai bauta.
בּוֹנֵה יְרוּשָׁלַ͏ִם יְהֹוָה נִדְחֵי יִשְׂרָאֵל יְכַנֵּֽס׃
3 Ya warkar da masu raunanar zuciya ya ɗaɗɗaura miyakunsu.
הָרֹפֵא לִשְׁבוּרֵי לֵב וּמְחַבֵּשׁ לְעַצְּבוֹתָֽם׃
4 Ya lissafta yawan taurari ya kuma kira kowannensu da suna.
מוֹנֶה מִסְפָּר לַכּוֹכָבִים לְכֻלָּם שֵׁמוֹת יִקְרָֽא׃
5 Shugabanmu mai girma ne mai iko duka; ganewarsa ba shi da iyaka.
גָּדוֹל אֲדוֹנֵינוּ וְרַב־כֹּחַ לִתְבוּנָתוֹ אֵין מִסְפָּֽר׃
6 Ubangiji yana kula da masu sauƙinkai yakan yar da mugaye a ƙasa.
מְעוֹדֵד עֲנָוִים יְהֹוָה מַשְׁפִּיל רְשָׁעִים עֲדֵי־אָֽרֶץ׃
7 Rera wa Ubangiji waƙar godiya; ku kada garaya ga Allahnmu.
עֱנוּ לַֽיהֹוָה בְּתוֹדָה זַמְּרוּ לֵאלֹהֵינוּ בְכִנּֽוֹר׃
8 Ya rufe sararin sama da gizagizai; yana tanada wa duniya ruwan sama yana kuma sa ciyawa tă yi girma a kan tuddai.
הַֽמְכַסֶּה שָׁמַיִם ׀ בְּעָבִים הַמֵּכִין לָאָרֶץ מָטָר הַמַּצְמִיחַ הָרִים חָצִֽיר׃
9 Yakan tanada wa shanu abinci da kuma saboda’ya’yan hankaki sa’ad da suka yi kira.
נוֹתֵן לִבְהֵמָה לַחְמָהּ לִבְנֵי עֹרֵב אֲשֶׁר יִקְרָֽאוּ׃
10 Jin daɗinsa ba ya a ƙarfin doki, balle farin cikinsa yă kasance a ƙafafun mutum;
לֹא בִגְבוּרַת הַסּוּס יֶחְפָּץ לֹא־בְשׁוֹקֵי הָאִישׁ יִרְצֶֽה׃
11 Ubangiji yakan yi farin ciki a waɗanda suke tsoronsa, waɗanda suke sa zuciya a ƙaunarsa marar ƙarewa.
רוֹצֶה יְהֹוָה אֶת־יְרֵאָיו אֶת־הַֽמְיַחֲלִים לְחַסְדּֽוֹ׃
12 Ki ɗaukaka Ubangiji, ya Urushalima; ki yabi Allahnki, ya Sihiyona.
שַׁבְּחִי יְרוּשָׁלַ͏ִם אֶת־יְהֹוָה הַֽלְלִי אֱלֹהַיִךְ צִיּֽוֹן׃
13 Gama yana ƙarfafa ƙyamaren ƙofofinki yana kuma albarkace mutanenki a cikinki.
כִּֽי־חִזַּק בְּרִיחֵי שְׁעָרָיִךְ בֵּרַךְ בָּנַיִךְ בְּקִרְבֵּֽךְ׃
14 Yana ba da salama ga iyakokinki yana kuma ƙosar da ke da alkama mafi kyau.
הַשָּׂם־גְּבוּלֵךְ שָׁלוֹם חֵלֶב חִטִּים יַשְׂבִּיעֵֽךְ׃
15 Yana ba da umarninsa ga duniya; maganarsa tana tafiya da sauri.
הַשֹּׁלֵחַ אִמְרָתוֹ אָרֶץ עַד־מְהֵרָה יָרוּץ דְּבָרֽוֹ׃
16 Yana shimfiɗa ƙanƙara kamar ulu yă kuma watsar da hazo kamar toka.
הַנֹּתֵן שֶׁלֶג כַּצָּמֶר כְּפוֹר כָּאֵפֶר יְפַזֵּֽר׃
17 Yana zuba ƙanƙara kamar ƙananan duwatsu. Wa zai iya jure wa sanyin da ya aiko?
מַשְׁלִיךְ קַֽרְחוֹ כְפִתִּים לִפְנֵי קָרָתוֹ מִי יַעֲמֹֽד׃
18 Yakan aiki maganarsa ta kuwa narkar da su; yakan tā da iskarsa, ruwaye kuwa su gudu.
יִשְׁלַח דְּבָרוֹ וְיַמְסֵם יַשֵּׁב רוּחוֹ יִזְּלוּ־מָֽיִם׃
19 Ya bayyana maganarsa ga Yaƙub, dokokinsa da ƙa’idodinsa ga Isra’ila.
מַגִּיד דְּבָרָו לְיַעֲקֹב חֻקָּיו וּמִשְׁפָּטָיו לְיִשְׂרָאֵֽל׃
20 Bai yi wannan ga wata al’umma ba; ba su san dokokinsa ba. Yabi Ubangiji.
לֹא עָשָׂה כֵן ׀ לְכׇל־גּוֹי וּמִשְׁפָּטִים בַּל־יְדָעוּם הַֽלְלוּ־יָֽהּ׃

< Zabura 147 >