< Zabura 146 >

1 Yabi Ubangiji. Yabi Ubangiji, ya raina.
Praise ye the LORD. Praise the LORD, O my soul.
2 Zan yabi Ubangiji dukan kwanakina; zan rera yabo ga Allahna muddin raina.
While I live will I praise the LORD: I will sing praises unto my God while I have any being.
3 Kada ka sa zuciyarka ga sarakuna, ga mutane masu mutuwa, waɗanda ba sa iya ceto.
Put not your trust in princes, [nor] in the son of man, in whom [there is] no help.
4 Sa’ad da numfashinsu ya rabu da su sai su koma ƙasa; a wannan rana shirye-shiryensu sun zama banza.
His breath goeth forth, he returneth to his earth; in that very day his thoughts perish.
5 Mai albarka ne wanda Allah na Yaƙub ne taimakonsa, wanda sa zuciyarsa yana a kan Ubangiji Allahnsa.
Happy [is he] that [hath] the God of Jacob for his help, whose hope [is] in the LORD his God:
6 Mahaliccin sama da ƙasa, teku, da kome da yake cikinsu, Ubangiji, wanda yake mai aminci har abada.
Which made heaven, and earth, the sea, and all that therein [is: ] which keepeth truth for ever:
7 Yakan biya bukatun mutanen da aka danne ya kuma ba da abinci ga mayunwata. Ubangiji yakan’yantar da’yan kurkuku,
Which executeth judgment for the oppressed: which giveth food to the hungry. The LORD looseth the prisoners:
8 Ubangiji yakan ba wa makafi ido, Ubangiji yakan ɗaga waɗanda aka rusunar da su ƙasa, Ubangiji yana ƙaunar masu adalci.
The LORD openeth [the eyes of] the blind: the LORD raiseth them that are bowed down: the LORD loveth the righteous:
9 Ubangiji yana tsaron baƙi yana kuma lura da marayu da kuma gwauruwa, amma yakan lalatar da hanyoyin mugaye.
The LORD preserveth the strangers; he relieveth the fatherless and widow: but the way of the wicked he turneth upside down.
10 Ubangiji yana mulki har abada, Allahnki, ya Sihiyona, daga zamani zuwa zamani. Yabi Ubangiji.
The LORD shall reign for ever, [even] thy God, O Zion, unto all generations. Praise ye the LORD.

< Zabura 146 >