< Zabura 145 >

1 Zabura ce ta yabo. Ta Dawuda. Zan ɗaukaka ka, ya Allahna, Sarki; zan yabi sunanka har abada abadin.
תהלה לדוד ארוממך אלוהי המלך ואברכה שמך לעולם ועד
2 Kowace rana zan yabe ka in kuma ɗaukaka sunanka har abada abadin.
בכל-יום אברכך ואהללה שמך לעולם ועד
3 Ubangiji da girma yake ya kuma cancanci yabo girmansa ya fi ƙarfin ganewar mutum.
גדול יהוה ומהלל מאד ולגדלתו אין חקר
4 Tsara guda za tă yi maganar ayyukanka ga wata tsara; za su yi magana game da manyan ayyukanka.
דור לדור ישבח מעשיך וגבורתיך יגידו
5 Za su yi zancen ɗaukakarka mai daraja, zan kuma yi tunani a kan ayyukanka masu banmamaki.
הדר כבוד הודך-- ודברי נפלאתיך אשיחה
6 Za su yi magana game da ikon ayyukanka masu bantsoro, zan kuma yi shelar manyan ayyukanka.
ועזוז נוראתיך יאמרו וגדלותיך (וגדלתך) אספרנה
7 Za su yi bikin yalwar alherinka suka kuma rera adalcinka da farin ciki.
זכר רב-טובך יביעו וצדקתך ירננו
8 Ubangiji mai alheri da kuma tausayi, mai jinkirin fushi cike kuma da ƙauna.
חנון ורחום יהוה ארך אפים וגדל-חסד
9 Ubangiji nagari ne ga duka; yana tausayin dukan abubuwan da ya yi.
טוב-יהוה לכל ורחמיו על-כל-מעשיו
10 Dukan abubuwan da ka yi za su yabe ka, ya Ubangiji; tsarkakanka za su ɗaukaka ka.
יודוך יהוה כל-מעשיך וחסידיך יברכוכה
11 Za su yi maganar ɗaukakar mulkinka za su kuma yi zancen ikonka,
כבוד מלכותך יאמרו וגבורתך ידברו
12 saboda dukan mutane su san manyan ayyukanka da ɗaukakar darajar mulkinka.
להודיע לבני האדם--גבורתיו וכבוד הדר מלכותו
13 Mulkinka madawwamin mulki ne, sarautarka kuma za tă dawwama cikin dukan zamanai. Ubangiji mai aminci ne ga dukan alkawuransa mai ƙauna kuma ga dukan abubuwan da ya yi.
מלכותך מלכות כל-עלמים וממשלתך בכל-דור ודר
14 Ubangiji yana riƙe da dukan waɗanda suka faɗi yana kuma ɗaga dukan waɗanda aka rusunar da su ƙasa.
סומך יהוה לכל-הנפלים וזוקף לכל-הכפופים
15 Idanun kowa yana dogara gare ka, kana kuma ba su abincinsu a lokacin da ya dace.
עיני-כל אליך ישברו ואתה נותן-להם את-אכלם בעתו
16 Ka buɗe hannunka ka kuma ƙosar da sha’awar kowane abu mai rai.
פותח את-ידך ומשביע לכל-חי רצון
17 Ubangiji mai adalci ne cikin dukan hanyoyinsa yana kuma nuna ƙauna ga dukan abubuwan da ya yi.
צדיק יהוה בכל-דרכיו וחסיד בכל-מעשיו
18 Ubangiji yana kusa da kowa da ya kira gare shi, ga duk wanda ya kira gare shi cikin gaskiya.
קרוב יהוה לכל-קראיו-- לכל אשר יקראהו באמת
19 Yakan cika sha’awar waɗanda suke tsoronsa; yakan ji kukansu yă kuma cece su.
רצון-יראיו יעשה ואת-שועתם ישמע ויושיעם
20 Ubangiji yakan lura da dukan waɗanda suke ƙaunarsa, amma dukan mugaye zai hallaka su.
שומר יהוה את-כל-אהביו ואת כל-הרשעים ישמיד
21 Bakina zai yi magana cikin yabon Ubangiji. Bari kowace halitta ta yabi sunansa mai tsarki har abada abadin.
תהלת יהוה ידבר-פי ויברך כל-בשר שם קדשו--לעולם ועד

< Zabura 145 >