< Zabura 144 >
1 Ta Dawuda. Yabo ya tabbata ga Ubangiji dutsena, wanda ya horar da hannuwana don yaƙi, yatsotsina don faɗa.
[By David.] Blessed be the LORD, my Rock, who teaches my hands to war, and my fingers to battle:
2 Shi ne Allah mai ƙaunata da kuma kagarata, katangata da mai cetona, garkuwata, wanda nake neman mafaka daga gare shi, wanda ya sa mutane a ƙarƙashina.
my loving kindness, my fortress, my high tower, my deliverer, my shield, and he in whom I take refuge; who subdues peoples under me.
3 Ya Ubangiji, wane ne mutum da ka kula da shi, ɗan mutum da har za ka yi tunaninsa?
LORD, what is man, that you care for him? Or the son of man, that you think of him?
4 Mutum yana kama da numfashi; kwanakinsa suna wucewa kamar inuwa.
Man is like a breath. His days are like a shadow that passes away.
5 Ka tsage sammanka, ya Ubangiji, ka sauko; ka taɓa duwatsu, domin su yi hayaƙi.
Part your heavens, LORD, and come down. Touch the mountains, and they will smoke.
6 Ka aiko da walƙiya ka watsar da abokan gāba; ka karɓa kibiyoyinka ka sa su gudu.
Throw out lightning, and scatter them. Send out your arrows, and rout them.
7 Ka miƙa hannunka daga bisa; ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni daga manyan ruwaye, daga hannuwan baƙi
Stretch out your hand from above, rescue me, and deliver me out of great waters, out of the hands of foreigners;
8 waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya, waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne.
whose mouths speak deceit, Whose right hand is a right hand of falsehood.
9 Zan rera sabuwar waƙa gare ka, ya Allah; a kan molo mai tsirkiya goma zan yi maka kiɗi,
I will sing a new song to you, God. On a ten-stringed lyre, I will sing praises to you.
10 ga Wannan wanda yake ba wa sarakuna nasara, wanda ya cece bawansa Dawuda. Daga takobin kisa.
You are he who gives salvation to kings, who rescues David, his servant, from the deadly sword.
11 Ka cece ni ka kuma kuɓutar da ni daga hannuwan baƙi waɗanda bakunansu sun cika da ƙarya, waɗanda hannuwansu na dama masu ruɗu ne.
Rescue me, and deliver me out of the hands of foreigners, whose mouths speak deceit, whose right hand is a right hand of falsehood.
12 Ta haka’ya’yanmu maza a ƙuruciyarsu za su zama kamar tsire-tsiren da aka kula da su,’ya’yanmu mata kuma za su zama kamar ginshiƙai da sassaƙa don adon fada.
Then our sons will be like well-nurtured plants, our daughters like pillars carved to adorn a palace.
13 Rumbunanmu za su cika da kowane irin tanadi. Tumakinmu za su ƙaru ninki dubu, ninki dubu goma-goma a filayenmu;
Our storehouses are full, filled with all kinds of provision. Our sheep bring forth thousands and ten thousands in our fields.
14 shanunmu za su ja kaya masu nauyi. Ba za a sami tashin hankali a katangarmu ba, ba zuwan zaman bauta, ba jin kukan damuwa a titunanmu.
Our oxen will pull heavy loads. There is no breaking in, and no going away, and no outcry in our streets.
15 Masu albarka ne mutanen da wannan zai zama haka; masu albarka ne mutanen da Allah ne Ubangiji.
Blessed are the people who are in such a situation. Blessed are the people whose God is the LORD.