< Zabura 143 >

1 Zabura ta Dawuda. Ya Ubangiji, ka ji addu’ata, ka saurari kukata don neman jinƙai; cikin amincinka da adalcinka ka amsa mini. 2 Kada ka gabatar da bawanka a gaban shari’a, gama babu wani mai rai da yake adali a gabanka. 3 Abokin gāba yana fafarata, ya murƙushe ni har ƙasa; ya sa ina zama a cikin duhu kamar waɗanda suka mutu tun tuni. 4 Ta haka ƙarfina ya ƙare a cikina zuciyata ta damu ƙwarai. 5 Na tuna da kwanakin baya na yi tunani a kan dukan ayyukanka na kuma lura da abin da hannuwanka suka yi. 6 Na buɗe hannuwana gare ka; raina yana jin ƙishinka kamar busasshiyar ƙasa. (Sela) 7 Ka amsa mini da sauri, ya Ubangiji; ƙarfina ya ƙare. Kada ka ɓoye fuskarka daga gare ni in ba haka ba zan zama kamar waɗanda suka gangara zuwa rami. 8 Bari safiya ta kawo mini maganar ƙaunarka marar ƙarewa, gama na sa zuciyata a gare ka. Ka nuna mini hanyar da zan bi, gama a gare ka na miƙa raina. 9 Ka cece ni daga abokan gābana, ya Ubangiji, gama na ɓoye kaina a gare ka. 10 Ka koya mini in yi nufinka, gama kai ne Allahna; bari nagarin Ruhunka yă bi da ni a ƙasar da ba gargaɗa. 11 Saboda sunanka, ya Ubangiji, ka kiyaye raina; a cikin adalcinka, ka fid da ni daga wahala. 12 A cikin ƙaunarka marar ƙarewa, ka rufe bakunan abokan gābana; ka hallaka dukan maƙiyana, gama ni bawanka ne.

< Zabura 143 >