< Zabura 141 >

1 Zabura ta Dawuda. Na yi kira gare ka, ya Ubangiji; ka zo da sauri. Ka ji muryata sa’ad da na yi kira.
[A Psalm by David.] YHWH, I have called on you. Come to me quickly. Listen to my voice when I call to you.
2 Bari a sa addu’ata a gabanka kamar turaren ƙonawa; bari ɗagawa hannuwana ta zama kamar hadayar yamma.
Let my prayer be set before you like incense; the lifting up of my hands like the evening sacrifice.
3 Ka sa mai tsaro a bakina, ya Ubangiji; ka yi tsaron ƙofar leɓunana.
Set a watch, YHWH, before my mouth. Keep the door of my lips.
4 Kada ka bar zuciyata ta juya ga yin abin da yake mugu, ta sa kai ga aikata mugayen ayyuka tare da mutane masu aikata mugunta; kada ka bari in ci abincinsu.
Do not incline my heart to any evil thing, to practice deeds of wickedness with men who work iniquity. Do not let me eat of their delicacies.
5 Bari mutum mai adalci yă buge ni, alheri ne; bar shi yă tsawata mini, mai ne a kaina. Kaina ba zai ƙi shi ba, duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka.
Let the righteous strike me, it is kindness; let him reprove me, it is like oil on the head; do not let my head refuse it; Yet my prayer is always against evil deeds.
6 Za a jefar da masu mulkinsu ƙasa daga ƙwanƙolin dutse, mugaye kuwa za su san cewa maganata daidai ne.
Their judges are thrown down by the sides of the rock. They will hear my words, for they are well spoken.
7 Za su ce, “Kamar yadda mutum kan yi huda yă tsage ƙasa, haka aka watsar da ƙasusuwanmu a bakin kabari.” (Sheol h7585)
"As when one plows and breaks up the earth, our bones are scattered at the mouth of Sheol." (Sheol h7585)
8 Amma na kafa idanuna a kanka, ya Ubangiji Mai Iko Duka; a cikinka ina neman mafaka, kada ka miƙa ni ga mutuwa.
For my eyes are on you, YHWH. In you, I take refuge. Do not leave my soul destitute.
9 Ka kiyaye ni daga tarkon da aka sa mini, daga tarkon da mugaye suka sa.
Keep me from the snare which they have laid for me, from the traps of evildoers.
10 Bari mugaye su fāɗa a cikin ragarsu, amma bari ni in zo in wuce lafiya.
Let the wicked fall together into their own nets, while I pass by.

< Zabura 141 >