< Zabura 140 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Ka cece ni, ya Ubangiji, daga mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici,
למנצח מזמור לדוד חלצני יהוה מאדם רע מאיש חמסים תנצרני׃
2 masu shirya maƙarƙashiya a zukatansu suna kuma kawo yaƙi kullum.
אשר חשבו רעות בלב כל יום יגורו מלחמות׃
3 Suna sa harsunansu su yi kaifi kamar na maciji; dafin gamsheƙa yana a leɓunansu. (Sela)
שננו לשונם כמו נחש חמת עכשוב תחת שפתימו סלה׃
4 Ka kiyaye ni, ya Ubangiji, daga hannuwan mugaye; ka tsare ni daga mutane masu rikici waɗanda suke shirin kwashe ni a ƙafafu.
שמרני יהוה מידי רשע מאיש חמסים תנצרני אשר חשבו לדחות פעמי׃
5 Masu girman kai sun sa mini tarko; sun shimfiɗa igiyoyin ragarsu sun kuma shirya mini tarko a hanyata. (Sela)
טמנו גאים פח לי וחבלים פרשו רשת ליד מעגל מקשים שתו לי סלה׃
6 Ya Ubangiji, na ce maka, “Kai ne Allahna.” Ka ji kukata ta neman jinƙai, ya Ubangiji.
אמרתי ליהוה אלי אתה האזינה יהוה קול תחנוני׃
7 Ya Ubangiji Mai Iko Duka, mai fansana mai ƙarfi, wanda yake garkuwoyin kaina a ranar yaƙi.
יהוה אדני עז ישועתי סכתה לראשי ביום נשק׃
8 Kada ka biya wa mugaye bukatunsu, ya Ubangiji; kada ka bar shirinsu su yi nasara, in ba haka ba za su yi fariya. (Sela)
אל תתן יהוה מאויי רשע זממו אל תפק ירומו סלה׃
9 Bari kawunan waɗanda suka kewaye ni su rufu da masifun da leɓunansu suka jawo.
ראש מסבי עמל שפתימו יכסומו׃
10 Bari garwashin wuta yă zubo a kansu; bari a jefar da su cikin wuta, cikin rami mai zurfi, kada su sāke tashi.
ימיטו עליהם גחלים באש יפלם במהמרות בל יקומו׃
11 Kada masu ɓata suna su taɓa kahu a ƙasar; bari masifa ta farauci mutane masu rikici.
איש לשון בל יכון בארץ איש חמס רע יצודנו למדחפת׃
12 Na san cewa Ubangiji ya shirya wa matalauta adalci yana kuma yi wa mabukata adalci.
ידעת כי יעשה יהוה דין עני משפט אבינים׃
13 Tabbatacce masu adalci za su yabi sunanka masu aikata gaskiya kuma za su zauna a gabanka.
אך צדיקים יודו לשמך ישבו ישרים את פניך׃

< Zabura 140 >