< Zabura 14 >

1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Wawaye sukan ce a ransu, “Ba Allah.” Sun lalace, ayyukansu kuwa mugaye ne; babu wani da yake yi abu mai kyau. 2 Ubangiji ya duba daga sama a kan’yan adam don yă ga ko akwai wani da ya gane, wani wanda yake neman Allah. 3 Duka sun kauce, duka gaba ɗaya sun zama lalatattu; babu ɗaya wanda yake yin abu mai kyau, ba ko ɗaya. 4 Masu aikata mugunta za su taɓa koyo. Suna cin mutane yadda mutane ke cin gurasa kuma waɗanda ba sa kira bisa Ubangiji? 5 Ga su, tsoro ya sha kansu, gama Allah yana cikin ƙungiyar adalai. 6 Ku masu mugunta kuna sa ƙoƙarin matalauta yă zama banza, amma Ubangiji ne mafakansu. 7 Kash, da ceton Isra’ila zai fito daga Sihiyona mana! Sa’ad da Ubangiji zai maido da sa’ar mutanensa, bari Yaƙub yă yi farin ciki Isra’ila kuma yă yi murna!

< Zabura 14 >