< Zabura 139 >
1 Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Ya Ubangiji, ka bincike ni ka kuwa san ni.
2 Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi; ka san tunanina daga nesa.
3 Ka san fitata da kuma kwanciyata; ka saba da dukan hanyoyina.
4 Kafin in yi magana da harshena ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.
5 Ka kewaye ni, gaba da baya; ka sa hannunka a kaina.
6 Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana, ya fi ƙarfi in gane.
7 Ina zan tafi daga Ruhunka? Ina zan gudu in tafi daga gabanka?
8 In na haura zuwa sammai, kana a can; in na yi gado a zurfafa, kana a can. (Sheol )
9 In na tashi a fikafikan safiya, in na sauka a gefe mai nisa na teku,
10 can ma hannunka zai bishe ni, hannunka na dama zai riƙe ni gam.
11 In na ce, “Tabbatacce duhu zai ɓoye ni haske kuma zai zama dare kewaye da ni,”
12 duhu ma ba zai zama duhu gare ka ba; dare zai haskaka kamar rana, gama duhu ya yi kamar haske gare ka.
13 Gama ka halicci ciki-cikina; ka gina ni gaba ɗaya a cikin mahaifar mahaifiyata.
14 Ina yabonka domin yadda ka yi ni abin tsoro ne da kuma abin mamaki; ayyukanka suna da banmamaki, na san da haka sosai.
15 Ƙasusuwana ba a ɓoye suke a gare ka ba sa’ad da aka yi ni asirce. Sa’ad da saƙa ni gaba ɗaya a zurfafan duniya.
16 Idanunka sun ga jikina marar fasali; dukan kwanakin da aka tsara mini a rubuce suke a littafinka kafin ɗayansu yă kasance.
17 Tunaninka suna da daraja gare ni, ya Allah! Yawansu ba su da iyaka!
18 A ce zan iya ƙirgansu, za su fi yashin teku yawa. Sa’ad da na farka, ina nan tare da kai har yanzu.
19 Da kawai za ka kashe mugaye, ya Allah! Ku rabu da ni, ku masu kisankai!
20 Suna magana game da kai da mugun nufi; maƙiyanka suna ɗaukan sunanka a banza.
21 Ba ina ƙin masu ƙinka ba, ya Ubangiji, ina kuma ƙyamar waɗanda suke tayar maka ba?
22 Ba ni da wani abu da nake musu sai kiyaye kawai; na ɗauke su abokan gābana.
23 Ka bincike ni, ya Allah ka kuma san zuciyata; ka gwada ni ka kuma san damuwata.
24 Duba ko akwai wani laifi a cikina, ka bishe ni a madawwamiyar hanya.