< Zabura 135 >
1 Yabi Ubangiji. Yabi sunan Ubangiji; yabe shi, ku bayin Ubangiji,
Praise Yahweh. Praise the name of Yahweh. Praise him, you servants of Yahweh,
2 ku waɗanda kuke hidima a gidan Ubangiji, cikin filayen gidan Allahnmu.
you who stand in Yahweh's house, in the courtyards of the house of our God.
3 Yabi Ubangiji, gama Ubangiji nagari ne; rera yabo ga sunansa, gama wannan yana da kyau.
Praise Yahweh, for he is good; sing praises to his name, for it is pleasant to do so.
4 Gama Ubangiji ya zaɓi Yaƙub ya zama nasa, Isra’ila ya zama mallakarsa mai daraja.
For Yahweh has chosen Jacob for himself, Israel as his possession.
5 Na san cewa Ubangiji yana da girma, cewa shugabanmu ya fi dukan alloli girma.
I know that Yahweh is great, that our Lord is above all gods.
6 Ubangiji yana yin abin da ya ga dama, a sammai da kuma a duniya, cikin tekuna da kuma cikin dukan zurfafansu.
Whatever Yahweh desires, he does in heaven, on earth, in the seas and all the ocean depths.
7 Yakan sa gizagizai su taso daga iyakokin duniya; yakan aika da walƙiya tare da ruwan sama ya fito da iska daga ɗakunan ajiyarsa.
He brings the clouds from far away, making lightning bolts accompany the rain and bringing the wind out of his storehouse.
8 Ya kashe’ya’yan fari na Masar,’ya’yan fari na mutane da na dabbobi.
He killed the firstborn of Egypt, both of man and animals.
9 Ya aiko da alamu da abubuwan banmamaki a tsirkiyarku, ya Masar, a kan Fir’auna da kuma dukan bayinsa.
He sent signs and wonders into your midst, Egypt, against Pharaoh and all his servants.
10 Ya bugi al’ummai masu yawa ya kuma karkashe manyan sarakuna,
He attacked many nations and killed mighty kings,
11 Sihon sarkin Amoriyawa, Og sarkin Bashan da kuma dukan sarakunan Kan’ana,
Sihon king of the Amorites and Og king of Bashan and all the kingdoms of Canaan.
12 ya kuma ba da ƙasarsa kamar abin gādo, abin gādo ga mutanensa Isra’ila.
He gave us their land as an inheritance, an inheritance to Israel his people.
13 Sunanka, ya Ubangiji, dawwammame ne har abada, sanin da aka yi maka, ya Ubangiji, yana nan cikin dukan zamanai.
Your name, Yahweh, endures forever; your renown, Yahweh, endures throughout all generations.
14 Gama Ubangiji zai nuna cewa mutanensa ba su da laifi ya kuma ji tausayin bayinsa.
For Yahweh defends his people and has compassion on his servants.
15 Gumakan al’ummai azurfa ne da zinariya, da hannuwan mutane suka yi.
The nations' idols are silver and gold, the work of men's hands.
16 Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani;
Those idols have mouths, but they do not speak; they have eyes, but they do not see;
17 suna da kunnuwa, amma ba sa ji, ba kuwa numfashi a bakunansu.
they have ears, but they do not hear, nor is there breath in their mouths.
18 Waɗanda suka yi su za su zama kamar su, haka kuma zai zama da dukan waɗanda suke dogara gare su.
Those who make them are like them, as is everyone who trusts in them.
19 Ya gidan Isra’ila, yabi Ubangiji; Ya gidan Haruna, yabi Ubangiji;
Descendants of Israel, bless Yahweh; descendants of Aaron, bless Yahweh.
20 Ya gidan Lawi, yabi Ubangiji; ku da kuke tsoronsa, yabi Ubangiji.
Descendants of Levi, bless Yahweh; you who honor Yahweh, bless Yahweh.
21 Yabo ya tabbata ga Ubangiji daga Sihiyona, gare shi wanda yake zama a Urushalima. Yabi Ubangiji.
Blessed be Yahweh in Zion, he who lives in Jerusalem. Praise Yahweh.