< Zabura 134 >
1 Waƙar haurawa. Yabi Ubangiji, dukanku bayin Ubangiji waɗanda kuke hidima da dare a gidan Ubangiji.
A song of degrees. Behold, praise ye the Lord, all ye seruants of the Lord, ye that by night stande in the house of the Lord.
2 Ku tā da hannuwanku a cikin wurinsa mai tsarki ku kuma yabi Ubangiji.
Lift vp your hands to the Sanctuarie, and praise the Lord.
3 Bari Ubangiji, Mahaliccin sama da ƙasa, ya albarkace ku daga Sihiyona.
The Lord, that hath made heauen and earth, blesse thee out of Zion.