< Zabura 133 >

1 Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Abu mai kyau ne, mai daɗi kuma sa’ad da’yan’uwa suna zaman lafiya!
שיר המעלות לדוד הנה מה טוב ומה נעים שבת אחים גם יחד׃
2 Yana kamar mai mai darajar da aka zuba a kai, yana gangarawa a gemu, yana gangarawa a gemun Haruna, har zuwa wuyan rigunansa.
כשמן הטוב על הראש ירד על הזקן זקן אהרן שירד על פי מדותיו׃
3 Yana kamar raɓar Hermon da take zubowa a kan Dutsen Sihiyona. Gama a can Ubangiji ya tabbatar da albarkarsa, har ma rai na har abada.
כטל חרמון שירד על הררי ציון כי שם צוה יהוה את הברכה חיים עד העולם׃

< Zabura 133 >