< Zabura 131 >

1 Waƙar haurawa. Ta Dawuda. Zuciyata ba mai girman kai ba ce, ya Ubangiji, idanuna ba sa fariya; ban dami kaina da manyan al’amura ba ko abubuwan da suka sha ƙarfina.
שיר המעלות לדוד יהוה לא-גבה לבי-- ולא-רמו עיני ולא-הלכתי בגדלות ובנפלאות ממני
2 Amma na haƙura na kuma kwantar da raina; kamar yaron da aka yaye tare da mahaifiyarsa, kamar yaron da aka yaye haka raina yake a cikina.
אם-לא שויתי ודוממתי-- נפשי כגמל עלי אמו כגמל עלי נפשי
3 Ya Isra’ila, sa zuciyarka ga Ubangiji yanzu da har abada kuma.
יחל ישראל אל-יהוה-- מעתה ועד-עולם

< Zabura 131 >