< Zabura 129 >
1 Waƙar haurawa. Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce,
2 sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba.
3 Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi.
4 Amma Ubangiji mai adalci ne; ya’yantar da ni daga igiyoyin mugaye.
5 Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya.
6 Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma;
7 da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa.
8 Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”