< Zabura 129 >

1 Waƙar haurawa. Sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, bari Isra’ila yă ce, 2 sun yi mini danniya ƙwarai tun ina ƙarami, amma ba su yi nasara a kaina ba. 3 Manoma sun nome bayana suka yi kunyoyinsu da tsayi. 4 Amma Ubangiji mai adalci ne; ya’yantar da ni daga igiyoyin mugaye. 5 Bari dukan waɗanda suke ƙin Sihiyona a juye da su baya da kunya. 6 Bari su zama kamar ciyawa a kan rufi, wadda takan bushe kafin tă yi girma; 7 da ita mai girbi ba ya iya cika hannuwansa, balle wanda yake tarawa yă cika hannuwansa. 8 Kada masu wuce su ce, “Albarkar Ubangiji ta kasance a kanku; muna sa muku albarka a cikin sunan Ubangiji.”

< Zabura 129 >