< Zabura 127 >

1 Waƙar haurawa. Ta Solomon. In ba Ubangiji ne ya gina gida ba, masu gininta suna wahala a banza ne. In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba, masu tsaro suna yin tsaro a banza. 2 Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna. 3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji, yara lada ne daga gare shi. 4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi haka’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya. 5 Mai albarka ne mutumin da korinsa sun cika da su. Ba za a kunyata su ba sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.

< Zabura 127 >