< Zabura 127 >

1 Waƙar haurawa. Ta Solomon. In ba Ubangiji ne ya gina gida ba, masu gininta suna wahala a banza ne. In ba Ubangiji ne yake tsaron birni ba, masu tsaro suna yin tsaro a banza.
所羅門上行之詩。 若不是耶和華建造房屋, 建造的人就枉然勞力; 若不是耶和華看守城池, 看守的人就枉然警醒。
2 Banza ne ka farka da wuri ka koma da latti, kana fama don abincin da za ka ci, gama yakan ba da barci ga waɗanda yake ƙauna.
你們清晨早起,夜晚安歇, 吃勞碌得來的飯,本是枉然; 惟有耶和華所親愛的,必叫他安然睡覺。
3 ’Ya’ya maza gādo ne daga Ubangiji, yara lada ne daga gare shi.
兒女是耶和華所賜的產業; 所懷的胎是他所給的賞賜。
4 Kamar kibiyoyi a hannun jarumi haka’ya’ya mazan da aka haifa wa mutum a ƙuruciya.
少年時所生的兒女 好像勇士手中的箭。
5 Mai albarka ne mutumin da korinsa sun cika da su. Ba za a kunyata su ba sa’ad da suke ƙarawa da abokan gābansu a ɗakin shari’a.
箭袋充滿的人便為有福; 他們在城門口和仇敵說話的時候, 必不至於羞愧。

< Zabura 127 >